Amurka ta soki China kan kin yarda da binciken asalin korona

A watan Mayu Shugaba Biden ya umarci jami'an leken asiri su ba shi rahoto kan asalin kwayar cutar cikin kwana 90

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A watan Mayu Shugaba Biden ya umarci jami'an leken asiri su ba shi rahoto kan asalin kwayar cutar cikin kwana 90

Amurka ta soki China kan kin yarda ta bar Hukumar Lafiya ta Duniya gudanar da bincike kan wasau daga cikin dakunan binciken kimiyyarta, a matsayin wani bangare na gano asalin kwayar cutar korona.

Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana matakin na gwamnatin China a matsayin abu na rashin sanin ya kamata kuma mai hadari.

Amurka ta soki China kan kin yarda ta bar Hukumar Lafiya ta Duniya gudanar da bincike kan wasau daga cikin dakunan binciken kimiyyarta, a matsayin wani bangare na gano asalin kwayar cutar covid-19.

Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana matakin na gwamnatin China a matsayin abu na rashin sanin ya kamata kuma mai hadari.

Masana kimiyya sun ce akwai alaka sosai tsakanin asalin bayyanar cutar da kasuwar da ake sayar da dabbobin ruwa a China

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masana kimiyya sun ce akwai alaka sosai tsakanin asalin bayyanar cutar da kasuwar da ake sayar da dabbobin ruwa a China

Tun a makon da ya gabata ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci da a gudanar da bincike kan dakunan gwajin kimiyya da cibiyoyin bincike a birnin Wuhan na China inda daga nan aka fara annobar korona.

China wadda har kullum take watsi da zargin da ake yi cewa mutum ne ya kirkiri kwayar cutar ta yi watsi da bukatar da hukumar ta WHO, da cewa rashin girmamawa ce da kuma girmankai.

To amma kuma Amurka wadda ta fi kowacce kasa samun mace-macen jama'a a sanadiyyar annobar, na matsa wa kan ganin China ta bayar da hadin kai an yi binciken.

Mataimakin ministan lafiya na China Zeng Yixin ya ce kasarsa ba za ta amince da sharuddan binciken ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mataimakin ministan lafiya na China Zeng Yixin ya ce kasarsa ba za ta amince da sharuddan binciken ba

A dangane da hakan ne mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, White House, Jen Psaki a wani taron manema labarai ta bayyana cewa yanzu ba lokaci ba ne da China za ta rinka kafewa da tirjiya kan batun.

Ta ce Amurka na son ta yi aiki tare da hukumomi da kasashen duniya domin matsa wa China lamba ta bayar da hadin kai ga binciken.

Psaki ta kara da cewa: ''Abin takaici matakin farko na binciken na WHO bai bayar da bayanai da hanya da ake gina sun wajaba daga China ba.

Amma goyon bayanmu ga gudanar da binciken ta fannoni daban-daban a wannan mataki na biyu, shin ne saboda za a yi shi ne sosai da sosai kuma ta kimiyya, musamman ma kuma cewa ba Amurka ce kadai ke son a yi binciken ba.''

Ta ce; ''abu ne da yake a fili China ba ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba.''

A watan Janairu na wannan shekarar masu bincike sun ziyarci birnin na Wuhan, inda aka fara ganin kwayar cutar a watan Disamba na 2019

Amma a farkon wannan watan shugaban Hukumar Lafiya ta Duniy Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya zayyana sharudan binciken na biyu, da suka hada da duba wasu cibiyoyin binciken kimiyya.

A watan Mayu Shugaba Biden ya yi kira ga jami'ansa kan su rubanya kokarinsu domin gano asalin kwayar cutar, yana mai cewa ra'ayin masu binciken sirri ya rabu kna ko ta faro daga dakin gwajin kimiyya ne ko kuma ta hanyar alakar mutum da wata dabba da ke da cutar ne.