Facebook na kashe mutane -Shugaba Biden

Shugaba Joe Biden

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Biden ya ce shafukan sada zumunta da muhawara irin su Facebook na hallaka mutane ta bari ana yada labaran karya kan rigakafin korona

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce shafukan sada zumunta da muhawara irin su Facebook suna kashe mutane, ta hanyar bari ana yada bayanan karya a kan alluran riga-kafin korona a shafukan.

Mista Biden ya fadi hakan ne, yayin da aka samu hauhawar masu kamuwa da korona a makon da ya gabata a kasar.

Sai dai kamfanin Facebook ya musanta zargin na Shugaba Biden da cewa shafin na samar da bayanai masu yawa da gamsarwa ga jama'a a kan annobar ta korona, fiye da duk wani shafi.

Shugaba Joe Biden ya fito fili ya yi wannan kakkausan suka ne da kuma zargin shafukan na sada zumunta da muhawara da Facebook na daya daga cikinsu da alhakin abin da ya ce kashe mutane ganin irin yadda annobar ta korona ke sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Abin da ya danganta da bayanan karya kan alluran riga-kafin cutar da ya ce shafukan na taimakawa wajen yadawa.

Akwai karerayi da dama da ake yadawa a kan alluran rigakafin korona
Bayanan hoto, Akwai karerayi da dama da ake yadawa a kan alluran rigakafin korona

Fadar shugaban ta soki kamfanonin shafukan na intanet da gaza yin abin ya kamata wajen yada labaran bogi a kan alluran riga-kafin koronar a shafukansu.

A lokacin da Mista Biden din ke barin fadar ne manema labarai suka tambaye shi sakon da yake da shi ga kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara, bai yi wata-wata ba sai ya musu wannan suka.

Ya ce ''Suna kashe mutane ne. Da gaske nake, ku duba ku gani, annobar da muke da kawai a tsakanin wadanda ba a yi musu rigakafi ba ne. Kuma suna kashe mutane.''

Sai dai Facebook ya fito fili ya kare kansa, inda shafin ya ce sama da mutane miliyan dubu biyu ne suka samu ingantattun bayanai a kan cutar ta korona da alluran riga-kafinta a shafukan, abin da ta ce ya fi na kowane shafi a intanet

Mista Biden ya yi zargin ne ganin irin yadda aka samu karuwar masu kamuwa da cutar , inda alkaluman suka kai har da kashi saba'in cikin dari a cikin satin da ya gabata a Amurkar.

Lamarin da ya sa hukumar yaki da cutuka ta kasar ta yi gargadin barkewar annobar a kan mutanen da ba a yi musu rigakafin ba, inda ake samun barkewar cutar a yankunan kasar da wadanda aka yi wa rigakafin ba su da yawa, irin su Florida.

Ana yi wa wata allurar rigakafin korona

Asalin hoton, Getty Images

Alkaluma sun nuna kashi casa'in da bakwai na wadanda aka kai asibti ba a yi musu rigakafin cutar ba.

Can a Las Vegas, jami'an kula da lafiya sun shawarci mutane da kowa, wanda aka yi wa rigakafi da wanda ba a yi masa ba, su tabbatar suna sanya takunkumi idan suna cikin taron mutane, saboda yadda ake samun karuwar masu cutar.

Hukumar yaki da cutuka ta Amurkar ta ce nau'in Delta na kwayar cutar ta korona shi ne yanzu ya fi bazuwa, inda yake ta haddasa mace-mace a fadin kasar, kuma kusan gaba daya a kan mutanen da ba a yi wa rigakafi ba.

Ita ma da take zargin shafukan sada zumunta da muhawara kan hauhawar annobar, mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurkar, Jen Psaki ta ce, kamfanonin shafukan kamar su Facebook har yanzu ba su tashi tsaye ba wajen hana sanya bayanan karya da batar da jama'a a kan rigakafin cutar ba a shafukansu.

Ta ce, muna fama ne da wani yanayi na mutuwa da rayuwa, saboda haka kowa yana da rawar da zai taka wajen tabbatar da bayar da bayanan gaskiya. A zahiri matakan da suka dauka ke nan.

Su kamfanoni ne na 'yan kasuwa, za su yanke shawara kan karin matakan da za su iya dauka. Abu ne da yake a zahiri akwai karin matakan da ya kamata a ce sun dauka.