Abin da ya tunzura ni na yi kalamai masu zafi a lokacin tafsiri – Alƙali Zaria

Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria

Asalin hoton, FB/Alkali Ustaz Abubakar

Bayanan hoto, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria
Lokacin karatu: Minti 4

Babban malamin addinin musuluci Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria, ya ce ya yi nadamar kalamansa da suka yi sanadin dakatar da shi daga gabatar da tafsirin azumin Ramadan a garin Damaturu na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Malamin wanda shi ne mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ta Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'ikamatus Sunnah (JIBWIS) mai hedikwata a Jos, ya shaida wa BBC cewa ya "karɓi dakatarwar" da aka yi masa da kaykkyawar niyya.

A ranar Litinin ne ƙungiyar izala mai shalkwata a garin Jos ta dakatar da malamin bayan tuhumarsa da yin kalaman da suka "saɓa wa dokokinta" na wa'azi, bayan kimanin kwana 11 yana tafsirin azumin Ramadan a garin Damaturu na jihar Yobe.

Gabanin watan Ramdana ne ƙungiyar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sani Yahya Jingir ta tura malamai 678 zuwa masallatai daban-daban a Najeriya da kuma ƙasashe masu maƙwaftaka domin gudanar da tafsirin Al-Qur'ani.

Sai dai yayin da azumin ya fara nisa, an ga faya-fayan bidiyon malamin na yawo a shafukan sada zumunta, inda yake sukar wasu shugabannin siyasa sanadiyyar matsalar tsaro da ake fama da shi a arewacin ƙasar.

A ɗaya daga cikin wadannan bidiyo an ji yadda ya ambato sunayen minista da gwamna da manyan ƴan siyasa yana sukar su saboda "gaza magance" matsalar tsaro da ake fama da ita a wane sashe na arewacin ƙasar.

A wani bidiyon kuma an ga malamin na sukar shugan ƙasar Bola Tinubu tare da zargin shi da gaza yin kataɓus wajen magance matsalolin ƙasar.

Abin da ya sa muka dakatar da Sheikh Alƙali - Izala

xxx

Asalin hoton, Jibwis NHQ Jos - Damaturu

A wani bayani da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Facebok, ta ce an dakatar da Alƙali Zaria ne bisa umarnin shugaban ƙungiyar na kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir saboda dalilai na tsaro.

Sanarwar da JIBWIS din ta fitar ta kuma ambato wasu dalilai guda uku da suka sa aka dakatar da malamin.

Daga ciki akwai:

  • Huɗubar da ya gabatar a hedikwatar 'yansanda da ke Damaturu a jihar ta Yobe.
  • Tafsirin da malamin ya yi sanye da kayan 'yan agaji a ranar Juma'a a masallacin Mokas, inda ya saba gabatar da karatun.
  • Nasihar da aka ambato cewa ya sake yi bayan sallar asuba a masallacin Alimarami a ranar Asabar.

JIBWIS ɗin ta ce duk da yake akwai matsalar tsaro a Najeriya kuma abu ne da ya shafi kowa, "amma salon da malamin ya bi wajen gabatar da wa'azin zai iya zama barazana ga tsaron Najeriya, kuma ya saɓa da koyarwar Izalar".

'Abin da ya harzuƙa ni'

A tattaunawar sa da BBC, Sheikh Alƙali Zaria ya ce shi kansa ya amince salon da ya bi wajen gabatar da tafsirin ya saɓa da koyarwar ƙungiyar Izala, kuma ya yi amanna cewa dakatar da tafsirin shi ne abin da ya fi dacewa.

"An min gargadi kafin dakatarwar, shi ɗan'adam ba wanda ya wuce wahami ya same shi," in ji malamin.

Alkali Zaria ya ce akwai abubuwan da suka tunzura shi har ya yi kalaman da ya yi.

"Abubuwan da suka tunzura ni, shi ne yadda na ga ake wulakanta ɗan'adam, ƴan bindiga suna dukan mutum, suna wulakanta su, ana dukan mata da bindiga, ana fasa musu kai," a cewar malamin.

Sai dai ya bayyana matakin da ƙungiyar ta ɗauka na dakatar da shi a matsayin abin da ya yi daidai.

Ya ce: "Ina biyayya ga shugabanci. Allah ya kaddara iyakar zaman da zan yi a Damaturu kenan".

Wane ne Alkali Abubakar Salihu Zaria?

Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria
Bayanan hoto, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria

An haifi Alƙali Abubakar Salihu Zaria ranar 1 ga watan Janairun 1980 a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a jihar Kaduna.

Ya fara karatu a makarantar Isah Abdulkarim Nursery and Primary School, kafin ya samu shaidar digirinsa ta farko a Jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanta fannin Addinin Musulunci.

Cikin malaman da ya yi karatu a hannunsu, akwai mahaifinsa da Mallam Umar a Tudun Wadan Zariya da Mallam Aminu Adam Nepu, masanin fiƙhu da nahawu, akwai Mallam Mai Bala'i Gyallesu da Mallam Shu'aibu Salihu Zaria.