Yadda masu niyyar zuwa Umrah daga Najeriya ke fargaba saboda yaƙin Iran

Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya maniyyata aikin umrah a ƙasar Saudiyya cikin watan Ramadan sun shiga halin rashin tabbas saboda yadda yaƙin da Isra'ila da Amurka ke yi da Iran ke neman ya shafi tafiyar su aikin.

Yaƙin na ci gaba da tilasta wa mahukunta rufe sufurin jiragen sama a wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya shafi ayyukan kamfanoni masu jigalar matafiya da kuma maniyyata aikin Umrah.

Miliyoyin musulmai ke halartar aikin Umrah a Saudiyya a cikin Ramadan, inda a 2025 kacal fiye da mutane miliyan 122 suka yi aikin, kamar yadda ƙidaddiga ta nuna.

Amma zaman ɗar-ɗar da aka shiga a Gabas ta tsakiya, wanda ya janyo rufe wasu muhimman filayen jirgin sama da ake bi domin jigilar maniyyata ya jefa ƴan Najeriya masu niyyar zuwa aikin Umrah na tuninin ko aikin ba zai yiwu ba.

Ƙasashen Iran da Iraq da Israel da Syria da Kuwait da Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa duk sun sanar da rufe filayen jirgin sama na ɗan wani lokaci bayan Amurka da Isra'ila sun ƙadaddar da jerin hare-hare kan Iran, lamarin da ya durƙusar da sufurin jirgin sama a Gabas ta Tsakiya.

Wannan lamari ya jefa fargaba a zukatan maniyyata daga Najeriya, saboda tsoron abin da zai iya hana su damar gudanar da wannan ibada.

Kawo yanzu dai hukumomin Saudiyya ba su sanar da rufe filayen jirgin saman ƙasar ba, amma akwai fargabar cewa hare-haren da Iran ke kai wa zasu iya shafar jigila zuwa ƙasa mai tsarki.

'Har yanzu ban cire ran zuwa umrah ba'

Tun daga lokacin da rikicin gabas ta tsakiya ya soma tafiye-tafiyen jirgen sama sun funkanci cikas. Wannan lamari dai ya haifar da gagarumin cikas ga maniyyata da ke shirin zuwa ko komawa gida daga Umrah a kasar Saudiyya, kuma babu tabbacin yuwar hakan muddin hare-haren da Amurka da Isra'ila da Iran suka ci gaba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alhaji Zaharaddeen Abubakar na daga cikin maniyyata da ke jiran zuwa umrah a kasar ta Saudiyya, ya kuma shaida wa BBC cewa fargabar su ba ta wuce yadda wasu sun riga sun kama ɗakuna kuma suna da duk takardun tafiya amma babu hali.

''Wanda ya ke can (Saudiyya)kuma, ya gama aikin ibadar shi zai dawo, idan jiragen da ke can ba za su tashi ba, ka ga shi ma abin fargaba ne,'' In ji Alhaji Zaharaddeen.

Sai dai ya jaddada cewa tunda aikin ibada ne, ba za a gajiya ba in dai aka samu dama.

Alhaji Zaharaddeen Abubakar ya kuma nemi hukumomi a Saudiyya su ɗauki mataki domin tabbatar da ganin Musulmai daga sassan duniya sun samu damar zuwa aikin Umrah ba tare da matsala ba.

Ya ce ''Lokacin aikin hajjin bara da ya wuce, a daidai lokacin an yi faɗa tsakanin Iran da Isra'ila, wanda maniyyata na Iran su ma sun samu itrin wannan matsala wanda Saudiyya ta ɗauki nauyin su tare da samar masu wajen zama, kuma hakan ya sa ba su samu wani ƙalubale ba har lokacin da aka dakatar da wannan yaƙin,

To yanzun ma fatan mu shi ne ya zama an samu kulawa ta musamman.''

'Wasu sun shiga jirgi amma ba su tashi ba'

Alhaji Musa Rabi'u Muhammed shi ne shugaban kamfanin da ke shirya tafiye-tafiye na Murna Travel Agency da ke jihar Kano a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa ''akwai mutanenmu wanda har sun shiga jirgi yana shirin tashi , amma dole aka dawo aka sauke su, yanzu haka suna gida.

''Duk wani jirgi wanda yake a nan gabas ta tsakiya, to wannan matsala ta shafe shi.'' in ji Alhaji Musa Rabi'u.

Ya ƙara da cewa a iya sanin shi babu wata fargaba a yanzu, amma a duk lokacin da ya faɗa a birnin Jiddah, nan fargaba ta ke.

Kawo yanzu dai wasu jiragen sun tashi daga ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Italiya da Switzerland, amma an soke tashin wasu jirage da dama.

Amurka da Isra'ila dai na ci gaba da kai munanan hare-hare a Iran.

Me ya sa Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran hari?

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce manufarsu ita ce "domin tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba."

"Za mu lalata makamansu da ƙona masana'antun haɗa makamansu da ke ƙarƙashin ƙasa. Wannan masana'anta sai an wayi gari babu ita,'' kamar yadda ya bayyana cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar.

Ya kuma gargaɗi gargaɗi dakarun Iran su ajiye makamansu domin samun "kariya" ko kuma su fuskanci mutuwa.

Trump ya buƙaci al'ummar Iran su tsara kansu da kyau ta yadda za su kifar da gwamnati, inda ya ce: "Idan mun gama ku ƙwace gwamnatinku. Wannan gwamnati za ta zama taku. Zai iya yiwuwa wannan ce dama ɗaya tal da za ku iya samu."

Wannan aikin soji da Amurka ta ƙaddamar, wanda ta yi wa laƙabi "Operation Epic Fury" ya zo ne bayan tsawon makonni Trump na barazanar ƙaddamar da yaƙi kan Iran idan ta ƙi amincewa da sabuwar yarjejeniyar nukiliya.

Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

Cibiyar tsara aikin sojin Amurka ta ce manufarta ita ce "lalata tsarin tsaron gwamnatin Iran, ta hanyar zaɓen wurare da suka fi zama barazana."

Daga farko, firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da "shirin kawar da abin da ke barazana ga wanzuwar ƙasarsa".

Iran ta bayyana harin da aka kai mata a matsayin "takalar faɗa kuma wanda ya saɓa wa doka" kuma ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a faɗin yankin.