An kakkaɓo makami mai linzami da ke kan hanyarsa zuwa Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images
Iran na ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marassa matuka kan asashe kamar Turkiyya da Isra'ila da Saudiyya da Kuwait.
Sai dai na'urorin kare sararin samaniya na ƙungiyar ƙawancen NATO sun kakkaɓo waɗanda ke wucewa ta Syria da Iraqi akan hanyarsu ta zuwa Turkiyya.
Qatar ta sanar da kakkaɓo makamai masu linzami da ke cin dogon zango guda biyu, sai dai ɗaya daga ciki ya faɗa sansanin soji da ke Al-Udaid.
An kuma kai hari sansanin sojin Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa, babu wanda ya jikkata ko hasarar rai.
Tuni Amurka ta rufe ofishin diflomasiyyarta na ƙasashen Saudiyya da Qatar da Lebanon.
















