Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 02/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 2 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 50 a Lebanon

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai a Lebanun sun ce sama da mutum 50 hare-haren makamai masu linzami da Isra'ila ta harba Tandem ya yi ajali a ƙasar.

    Sama da mutum 150 sun jikkata, a abin da suka kira ramuwar gayya kan goyon bayan Iran da kasar ke yi.

    Isra'ila ta ce ta kai harin ne a birnin Beirut, kan duk wani mai alaƙa da ƙungiyar Hezbollah da mayaƙan jihadi na Falasɗinu.

    Rahotanni sun bayyana cewa dubban farar hula ne suka sterewa muhallansu a kudancin Lebanun. Tun da fari ƙungiyar Hezbollah ta kai hare-haren makaman roƙa da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila bayan kisan jagoran addinin Iran Ayatullah Ali Khamenei.

  2. Farashin mai da gas ya tashi a kasuwannin duniya

    Gas

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin man fetru da iskar gas ya yi tashin gwauron zaɓo a kasuwannin duniya bayan ɓarkewar hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran da kuma na ramuwar gayyar da Iran da ƙaddamar a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yaƙin ya haifar da tsaikon haƙar mai da iskar gas a rijiyoyin haƙar man a faɗin hyankin gabads ta Tsakiya da dakar da jigilar man daga mashigar Hormuz.

    Da safiyar yau Litinin farashin man fetur samfurin Brent ya tashi da kashi 13 cikin 100, inda ya kai dala 37.82 kan kowace ganga, mafi tsada da ya kai tun watan Janairun 2025.

    Haka ma man feter na Amurka, samfurin West Texas ya ƙaru da kashi fiye da 12 cikin 100, inda ya kai dala 33.75 kowace gangan, mataki mafi tsada da ya kai tun watan Yuni.

  3. An samu rahotonnin mummunar fashewa a birnin Beruit

    Hoto hayaƙi na tashi daga wani birni

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotonni daga Lebenon sun ce an ji ƙarar wata babbar fashewa a birnin Beirut.

    Bayanai sun ce fashewar ta auku ne a unguwar Dahieh da ke tsakiyar babban birnin ƙasar, matattarar mayaƙan ƙungiyar Hezbollah

    An riƙa jin sanarwa ta na'urorin amsa kuwwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke Awkar, inda ake bai wa ma'aikatan ofishin jakandancin umarnin ɓuya tare da kauce wa tsayawa kusa da taga.

  4. Mun shirya wa dogon yaƙi da Amurka - Iran

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian

    Sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani ya ce ƙasar a shirye take don gwabza yaƙi mai tsawo saɓanin Amurka.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ya ce fiye da shekara 300 Iran ba ta taɓa tsokano faɗa ba, kuma dakarun sojinmu ba su taɓa shiga wani yaƙi ba sai na kare kai.

    ''Don haka duk abin da zai faru, za mu kare kanmu, kuma za mu yi amfani da kafuwar daularmu na tsawon shekara 6,000 don tabbatar da ganin maƙiya ba su samu nasara a kanmu ba'', kamar yadda ya wallafa.

    Tun da farko sakataren tsaron Amurka ya bayyana a wani taron manema labarai cewa harin da Amurka ta ƙaddamar a Iran har abada ba ne.

    ''Maƙasudinsa shi ne lalata makaman linzamin ƙasar da rundunar sojin ruwanta da sauran kayayyakin sojin ƙasar'', in ji shi.

  5. Labarai da dumi-dumi, Iran ta tabbatar da mutuwar mai ɗakin Khamenei

    Gidan talbijin na Iran ta tabbatar da kisan mai ɗakin jagoran addinin Iran, Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh.

    Kafar yaɗa labaran Hamshahri ta ruwaito cewa Mansoureh ta ji munanan raunuka tun a ranar farko ta hare-haren Amurka ta Isra'ila a ƙasar.

    Tun da farko an bayar da rahoton kisan Zahra Haddad Adel mai ɗakin Mojtaba Khamenei ɗa ga jagoran addinin, da kuma wata surikar jagoran, da jikarsa, Zahra Mohammadi Golpayegani.

  6. Isra'ila ta ce ta kashe manyan jami'an leƙen asirin Iran

    Rundunar sojin Kisra'ila ta ce ta kashe wasu manyan jami'an leƙen asirin Iran.

    Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun ce harinsu na ranar Asabar ya kashe babban mataimakin ministan leƙen asirin ƙasar, Yahya Hamidi.

    haka ma sojojin na Isra'ila sun ce sun kashe shugaban sahen tattara bayanan sirri na Iran, Jalal Pourhossein,tare da wasu manyan jami'an ma'aikatar.

    Kawo yanzu Iran ba ta ce komai ba game da wannan iƙirari.

  7. Ƴan shi'ar Najeriya sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Iran

    ƴan shi'a

    Asalin hoton, Media Forum of the Islamic movement

    Ƙungiyar mabiya aƙidar Shi'a ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayanta ga jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa ƙasar.

    Jagoran shi'a

    Asalin hoton, Media Forum of the Islamic movement

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce mabiyanta sun gudanar da zanga-zangar a biranen Abuja da Zariya da Illela da Kaduna da Kano da Jigawa da Bauchi da Azare da Potiskum da Minna da Katsian da Yola da sauransu.

    ƴan shi'a

    Asalin hoton, Media Forum of the Islamic movement

    Ƙungiyar ta ce ta kuma riƙa gudanar da addu'o'in neman nasara ga Iran.

    ƴan shi'a

    Asalin hoton, Media Forum of the Islamic movement

    Haka ma ƴan ƙungiyar sun ce sun jajanta wa al'ummar Musulman duniya, musamman Iraniyawa kan mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

    Ƴan shi'a

    Asalin hoton, Media Forum of the Islamic movement

  8. 'Babu alamun yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran illa'

    ...

    Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

    Shugaban hukumar da ke sanya ido kan makamin nukiliya (IAEA), Rafael Grossi, ya ce babu wani alamar da ke nuna cewa an yi illa ko lahani ga ɗaya daga cikin cibiyoyin nukiliyar Iran, ciki har da cibiyar Bushehr da sauran wuraren sarrafa makamashin nukiliya.

    Cikin wani jawabi ga kwamitin masu kula da harkokin nukiliya, Mista Grossi ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin tuntuɓar hukumomin kula da nukiliyar Iran amma har yanzu ba a samu nasarar yin hakan ba.

    Ya yi kiran mayar da hankali sosai ga duk wani aiki na soja, la’akari da cibiyoyin nukiliya da ke Iran da sauran ƙasashen yankin, ciki har da Bahrain da Iraq da Kuwait da Oman da Qatar da Saudi Arabia.

    Jakadan Iran a hukumar IAEA, Reza Najafi, ya shaida wa BBC cewa an kai hari cibiyar nukiliya ta Natanz a ranar Lahadi, amma bai bayar da ƙarin bayani ba.

  9. Iran ta ce ta kai hari ofishin Netanyahu

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ambato kakakin rundunar dakarun juyin juya hali na ƙasar na cewa an kai hari ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma shalkwatar rundunar sojin saman ƙasar.

    Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce ''nan gaba kaɗan ne za ta bayyana ɓarnar da hare-haren suka yi'', kamar yadda sashen Fasha na BBC ya ruwaito.

    Sai dai kawo yanzu ofishin Netanyahun bai ce komai ba game da batun.

  10. Mun kai wa Isra'ila hari da makami mai linzami na Khyber - Iran

    makami

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta ce ta yi amfani da makaminta mai linzami na Khyber wajen kai hare-haren da ta kai Isra'ila.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar, Rundunar IGRC ta ce a hare-harenta kan Isra'ila na baya-bayan nan ta kai hari biranen Tel Aviv da Haifa da Gabashin Birnin Kudus.

    Makami mai linzami na Khyber na da ƙarfin da zai iya yion tafiyar kilomita 2,000.

    Makami

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin babban hafsan sojojin ƙasar, Mohammad Reza Ashtiani ya bayyana makamin a matsayin ɗaya daga cikin makamai masu linzami na zamani da wani kamfanin ƙasar ya ƙera da manyan kawunan da zai iya ɗaukar abubuwan fashewa masu nauyin kilogiram 1,500.

    Haka ma sojojin Iran ɗin sun ce sun kai hare-hare kan sansanin sojin saman Amurka na Ali al-Salem da ke ƙasar Kuwait da kuma wani jrigin ruwa a tekun Indiya.

  11. An kai wa matatar man Saudiyya hari da jirage marasa matuƙa

    Hayaƙi

    Asalin hoton, Social media

    Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da harin jirage marasa matuƙa kan matatan manta.

    Saudiyyar ta ce ta samu nasarar daƙile wutar da ta tashi a matatar bayan kakkaɓo jiragen marasa matuƙa.

    Ma'aikatar makamashin ƙasar, ta ce an samu nasarar kashe wutar da ta matatar mai ta Ras Tanura - wanda kamfanin man ƙasar Aramco ke gudanarwa

    Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran ƙasar ya wallafa, ya ce wutar ta yi wa matatar ''ƙaramar illa saboda ɓaraguzan'' jiragen da aka kakkaɓo sun faɗa wasu wurare.

    Yana mai cewa jami'an kashe gobara sun samu nasarar gaggauta kashe wutar.

    Wani bidiyo da BBC ta tantance ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe a saman matatar.

    Saudiyya ta daɗe tana bai wa dakarun Amurka da na ƙasashen Yamma mafaka a ƙasarta, kuma a ranar Asabar gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar Allah wadai kan hare-haren Iran.

  12. Najeriya ta yi kiran kai zuciya nesa a yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa kan rikicin da ke ƙaruwa a ƙasashen yankin Gulf wanda zai iya haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki ɗaya inda ta yi kiran kai zuciya nesa.

    Cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su kwantar da hankali tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya ƙara ta'azara rikicin.

    Sanarwar ta kuma jaddada mahimmancin fifita tattaunawa da fahimtar juna fiye da faɗa da rikici, tare da bin ƙa’idojin da Majalisar Ɗinkin Duniya da Yarjejeniyar Geneva suka shimfiɗa, musamman wajen mutunta ikon ƙasashe, da martaba iyakokinsu.

    "Najeriya na kiran rage amfani da ƙarfi saboda kare rayukan fararen hula da kauce wa duk wani mataki da zai iya karya ƙa’idojin da dokokin duniya," in ji sanarwar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga duk wani yunƙuri na diflomasiyya da ake yi a tsarin ƙasa da ƙasa da kuma na yankin don warware rikicin.

    Haka kuma giwar Afirkan ta ce za ta yi maraba da duk wasu matakai na gina amincewa da shiga tsakani, da tattaunawa tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.

  13. Jiragen yaƙin Amurka sun faɗi a Kuwait

    ...

    Ma’aikatar tsaron Kuwait ta bayyana cewa wasu jiragen yaƙin Amurka sun fadi a safiyar yau a ƙasar.

    An tabbatar cewa ma’aikatan jiragen sun tsira ba tare da wata rauni ba, an kuma kai su asibitoci domin a duba lafiyarsu, inda aka tabbatar cewa suna cikin yanayi mai kyau.

    Ma’aikatar ta ce tana haɗin gwiwa da Amurka wajen gano abin da ya janyo hatsarin jiragen, sannan kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin lamarin.

    Har yanzu babu jawabi daga rundunar sojin Amurka, wadda ke jagorantar ayyukan sojin ƙasar a yankin, game da faduwar jiragen a Kuwait.

    Sai dai Ma’aikatar Tsaron Kuwait ta sanar cewa jiragen yaƙin Amurka da dama sun fadi a ƙasar.

    Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da rikici ke ƙaruwa da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda Iran ke kai hari kan manyan wuraren sojojin ƙasashen ƙetare a matsayin ramuwar gayya bayan farmakin da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran.

  14. Ba za mu ce komai zai tafi daidai ɗari bisa ɗari ba a zaɓen 2027 - Shugaban Inec

    ....

    Asalin hoton, Joseph Ayo Babalola University

    Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, Joash Amupitan ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa hukumar na da ƙarfin aika sakamakon zaɓe ta na’ura a zaɓen 2027, amma ba zai iya tabbatar da cewa komai zai tafi daidai ɗari bisa ɗari ba.

    Amupitan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi yayin wani taron jin ra'ayin jama’a, inda ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su rage tsammani mai yawa, yana cewa hukumar za ta yi iya ƙoƙarinta wajen gudanar da sahihin zaɓe amma ba za a iya cewa ba za a samu wata matsala ba.

    Ya jaddada cewa “zaɓe ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya, kuma ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a da gaskiya a hukumomi na da matuƙar muhimmanci.”

    Shugaban INEC ya ƙara da cewa hukumar na da damar tura sakamakon zaɓe ta na’ura, amma babban ƙalubalen shi ne batun aikawa kai tsaye a lokaci guda.

  15. Trump ya yi gargaɗin samun ƙarin mutuwar dakarun Amurka a yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta, sannan ya bayyana a wasu kafafen watsa labarai, inda ya shaida wa jama’ar Amurka cewa ya kamata su kasance cikin shirin yiwuwar samun karin mace macen dakarun ƙasar a yaƙin da suke yi da Iran.

    An tabbatar da mutuwar sojoji uku zuwa yanzu, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka.

    Da yake magana da NBC, Trump ya ce hare haren da aka kai wa Iran sun zama dole, kuma za su iya shafe aƙalla wata guda.

    A wani saƙo da ya aika wa dakarun rundunar juyin-juya halin Iran, Mista Trump ya bukaci su yi saranda, ko su fuskanci mutuwa.

  16. Farashin mai ya tashi a kasuwanni duniya saboda yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya tashi da kashi goma cikin ɗari yayin da kasuwannin makamashi a Asiya suka buɗe a ranar Litinin, ƙari mafi yawa da aka samu tsawon watanni.

    Wannan yana nuna haɗarin da ke tattare da jigilar mai ta Mashigin Hormuz da Iran ta ba da sanarwar rufewa.

    Tuni ƙasashen duniya suka fara shirin tunkarar sakamakon da ke tattare da hakan, la'kari da cewa ta nan ne ake wucewa da aƙalla kashi 20 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a duniya ciki har da man fetur.

    Rahotanni sun ce dakarun sojin ruwan Iran na kai hari kan dukkan jiragen ruwan da suka nemi kangarewa umarninsu na ja da baya, harma sun lalata wasu jiragen dakon mai uku.

    Kasuwannin hannayen jari da suka buɗe da safiyar nan a Asiya sun fadi warwas. Akwai fargabar cewa rikicin da ke ci gaba da faruwa zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.

  17. Hare-haren Isra’ila sun kashe aƙalla mutum 31 a Lebanon

    ....

    Hare-haren sama da Isra’ila ta kai kan Beirut da kudancin Lebanon sun kashe mutum 31 tare da jikkata 149, a cewar ma’aikatar lafiya ta ƙasar yayin da rikici ke ƙaruwa a Yankin Gabas ta Tsakiya

    Sanarwar ta ce adadin na wucin gadi ne kuma ana ci gaba da tantancewa.

    Babban hafsan rundunar sojin Isra’ila, Eyal Zamir, ya bayyana cewa sojojin sun fara wani farmaki da ya kira “gagarumin shiri” kan ƙungiyar Hezbollah wanda zai iya ɗaukar kwanaki da dama.

    Tashin hankalin yankin ya ƙaru ne sakamakon rikicin kashe jagaron addinin Iran Ayatollahi Khamenei a hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai Iran.

    Rikicin da ake ciki yanzu na ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya, musamman saboda fargabar cewa faɗa zai iya bazuwa zuwa cikakken yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

  18. Yadda Amurka da Isra'ila suka kwashe watanni suna kitsa kashe Ayatollah Khamenei

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kisan da aka yi wa Jagoran Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya faru ne da safe, ba da tsakar dare ba, kamar yadda wasu za su yi tsammani.

    Hakan ya faru ne saboda Amurka da Isra'ila sun yi amfani da wani bayanin sirri da ya zo musu ƴan awanni kafin lokacin.

    Tsawon watanni, Amurka da Isra'ila sun riƙa dakon lokacin da manyan jagororin Iran za su haɗu wuri ɗaya, daga nan sai suka fahimci cewa Khamenei zai halarci wani gida a tsakiyan birnin Tehran da safiyar ranar Asabar.

    Haka nan kuma sun gano wani wurin da manyan sojoji da jami'an tattara bayanan sirri suke yin wata ganawa a daidai wannan lokacin.

    Tsawon watanni, Amurka da Isra'ila sun riƙa bibiyar duk wani motsi na jagoran addinin na Iran.

    Hanyar da suka yi hakan abu ne na sirri, duk da dai shugaban Amurka Donald Trump ya ɗan bayar da satar amsa a bayanin da ya wallafa a shafin sada zumunta.

    "Ya gaza zulle wa bayananmu na sirri da kuma nagartaccen tsarin bibiyar da muka yi amfani da shi."

    Wannan zai iya zama mutum ne ke ba su bayanai ko kuma wata fasaha ta bibiyar jami'an Iran.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.