Covid-19: Abin da ya kamata ku sani game da nau'in Delta na cutar korona

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Hukumomi a Najeriya sun roki 'yan kasar su rika bin dokokin kariya daga cutar korona

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya, NCDC, ta ce an gano nau'in cutar korona mai suna Delta mai saurin bazuwa a ƙasar.

Wata sanarwa da Hukumar ta fitar ranar Alhamis ta ce an gano nau'in ne a Lagos a jikin wani matafiyi da ya je ƙasar.

"Ganin yadda nau'in na Delta yake yaduwa da kuma gano shi a Najeriya, NCDC ta bukaci 'yan Najeriya su tabbatar sun bi matakan kare lafiya da kuma na yin nesa-nesa da juna da aka riga aka ayyana," a cewar sanarwar.

Nau'in na Delta ya watsu a kasashe fiye da 90 kuma ana sa ran zai ci gaba da yaduwa a kasashe da dama.

Yaya nau'in delta yake?

Ba wani sabon abu ba ne idan kwayar cutar bairos ta hayayyafa da sauya tsarin halittarta a yayin da take yaduwa, kuma tuni masana kimiyya suka yi gargadin cewa wasu nau'ukan masu ban tsoro za su iya bijirowa.

Ko da yake har yanzu ba a kai ga sanin yadda yake yaduwa ba, amma bincike ya nuna cewa nau'in na delta yana da karin hatsari da ke tattare da yadda yake yaduwa cikin sauri.

A watan Mayu Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ayyana nau'in na delta a matsayin "nau'in da ya kamata ya sanya damuwa".

Ana ayyana nau'in bairos a matsayin wanda ya kamata a damu da shi sosai ne idan akwai karin shaidu da ke nuna cewa nau'in ya fi saurin yaduwa, yana kuma haifar da cutuka masu zafi sannan yana rage karfin tasirin riga-kafi da magunguna.

Shin nau'in delta yana haddasa karin cutuka masu zafi ko alamominsu?

Ana bukatar gudanar da karin bincike kan nau'in na delta, amma akwai alamu da ke nuna cewa nau'in na delta yana iya haddasa cutuka masu zafin gaske.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta The Lancet ranar 14 ga watan Yuni ya yi nazari kan tasirin nau'in delta a Scotland, inda ya mamaye.

Masu bincike sun gano cewa kasadar kwantar da mutumin da ya kamu da nau'in delta na cutar korona ta ninka idan aka kwatanta da wanda ya kamu da nau'in alpha.

Kazalika masu bincike a Birtaniya sun gano cutar korona nau'in delta take da alamomi daban da na nau'in da aka fi sani.

Bayanai sun nuna cewa masu fama da nau'in delta suna nuna alamomin da suka hada da ciwon kai, bushewar makogwaro, majina da kuma zazzabi — irin wanda mutumin da ya kamu da mura yake fama da shi.

Karin bayani kan coronavirus

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Karin bayani kan coronavirus

Asalin hoton, NCDC