Arsenal da Man United na gogayya kan Gomes, PSG da Barcelona kan Diaz

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta yi gogayya da Manchester United wajen sayen dan wasan tsakiya na Wolves da Brazil Joao Gomes, mai shekara 23, a bazaran nan. (O Dia)
Paris St-Germain da Barcelona na son dan wasan gaba na Liverpool da Colombia Luis Diaz, wanda a kwanannan wakilinsa ya ziyarce shi. (Telegraph)
Tottenham na sa ido a kan dan wasan gaba na Athletic Bilbao Nico Williams, na Sifaniya mai shekara 21 wanda yake da damar sayar da shi a kwantiraginsa a kan fam miliyan 42.8. (Telegraph)
Sai dai Williams din zai iya ci gaba da zama tsawon wata kaka a Athletic Bilbao kafin Barcelona ta nemi sayensa a bazarar 2025. (Sport)
Ana samun cigaba sosai a tattaunawar Newcastle United da dan wasanta na tsakiya Joelinton, kuma dan wasan na Brazil na dab da sanya hannu a wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar. (Telegraph)
Ana sa ran dan bayan Faransa Raphael Varane, mai shekara 30, da kuma dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 32, su kasance gaba-gaba a jerin 'yanwasan da Manchester United za ta rage a bazara. (Talksport)
A shirye Liverpool take ta bar Mohamed Salah ya tafi gasar Saudiyya a bazaran nan, idan har dan wasan na Masar ya bukaci barin Anfield. (HITC)
Manchester City na sha'awar dan wasan gaba na gefe na Wolves Pedro Neto to amma fa kungiyar za ta iya fuskantar gogayya da kungiyoyin Saudiyya, a kan dan wasan na tawagar Portugal. (Teamtalk)
Crystal Palace da Fulham na nazarai kan zawarcin dan bayan Union Berlin Danilho Doekhi, na Holland. (Football Insider)
Dan gaban Real Madrid Rodrygo, na Brazil, ya ce ya yi watsi da tayin tafiya Liverpool a 2017, duk da cewa kungiyarsa a lokacin Santos ta amince da tayin yuro miliyan uku da Liverpool ta yi masa. (90 Min)
Dan bayan Bayer Leverkusen Jeremie Frimpong, na tawagar Holland mai shekara 23, na daukar hankalin Liverpool inda take zawarcinsa, da zai kai ga mayar da Trent Alexander-Arnold zuwa dan wasan tsakiya idan cinikinsa ya tabbata. (Football Insider)
Har yanzu Manchester United da Newcastle ba su cimma matsaya ba a kan abin da United din za ta bayar a kan Dan Ashworth, kuma watakila sai kungiyar ta Old Trafford ta jira zuwa wasu watanni kafin ta nada shi a matsayin sabon darektanta na wasanni. (Guardian)














