Liverpool na tattaunawa kan Amorim, Man Utd na zawarcin Konsa

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na tattaunawa da kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim, mai shekara 39, domin ya maye gurbin Jurgen Klopp a Anfield. (Foot Mercato - in French)
Barcelona ma ta nuna matsuwarta kan kocin na Portugal sai dai da alama ta janyesaboda tunanin zai zabi tafiya Ingila. (Sport - in Spanish)
Manchester United na kuma duba yiwuwar gwada sa'arta kan ɗan wasan Aston Villa Ezri Konsa, mai shekara 26. (Football Transfers)
Ɗan wasan gaba a Portugal Joao Felix ya ce abokinsa da suke kasa guda Bernardo Silva, na son komawa Barcelona. (Gerard Romero)
Atalanta ta ce babu wanda ya tuntubeta daga Liverpool kan dan wasanta Teun Koopmeiners mai shekara 26. (90min)
Liverpool na son saye ɗan wasan Uruguay Federico Valverde, mai shekara 25 daga Real Madrid. (Teamtalk)
Mai bugawa Bologna da Netherlands gaba, Joshua Zirkzee mai shekara 22, ya kasance wana Manchester United da Liverpool ke hari. (Mirror)
Arsenal za ta kalubalanci Manchester United a cinikin ɗan wasan Barcelona mai shekara 19 da Senegal Mikayil Faye. (Calciomercato, via TeamTalk)
Manchester United ta gabatar da tayi kan dan wasan Ingila Bendito Mantato. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Portugal Marco Silva, mai shekara 46, ya ja hankalin West Ham. (Sun)
Everton na fuskantar ragin maki bayan fitar da bayanai kan kudaden asusunta.(Football Insider)











