Man U za ta sake taya Branthwaite, Crystal Palace ta ƙi sallama Guehi

Jarrad Branthwaite

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jarrad Branthwaite
Lokacin karatu: Minti 3

Manchester United ta fara shirin sake zawarcin dan wasa mai tsaron bayan Ingila da Everton Jarrad Branthwaite mai shekara 22 bayan da ta samu labarin cewa sabon dan wasan Faransa Leny Yoro dan shekaea 18 da ta dauko a baya baya nan ba zai iya taka leda a bana ba . (Sun), external

Ana sa ran dan wasa mai tsaron bayan Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 24, da dan wasan bayan Morocco Noussair Mazraoui, mai shekara 26, za su koma Manchester United daga Bayern Munich yayin da ake ci gaba da samun ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin kungiyoyin biyu. (Sky Sports Germany), external

Bayern Munich ta janye daga cinikin sayan dan wasan baya na Jamus Jonathan Tah mai shekara 28 daga Bayer Leverkusen. (Kicker - in German), external

Crystal Palace ta yi watsi da tayi na biyu, wanda aka yi ammanar cewa ya kai fam miliyan 50 da Newcastle United ta yi mata kan dan wasan tsakiyar baya Marc Guehi, mai shekara 24, yayin da aka ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu. (Sky Sports), external

Hamshakin attajirin nan na Amurka John Textor ya yi yunkurin zama mai kaso mafi yawa a hannayen jarin Everton abinda kuma zai kawo karshen cece-kucen da ake yi akan sayar da kungiyar (Guardian), external

Dan wasan gaba na Brazil Rodrygo, mai shekara 23,ba shi da niyyar barin Real Madrid ko da Manchester City ta yi kokarin daukarsa domin maye gurbin dan wasan Argentina mai kai hari Julian Alvarez, wanda ke shirin komawa Atletico Madrid. (AS - in Spanish), external

Crystal Palace na tattaunawa da Galatasaray a kan kwantiragin tsawon kakar wasa kan tsohon dan wasan gefe na Eagles Wilfried Zaha. Dan wasan kasar Ivory Coast mai shekara ya bar Selhurst Park domin komawa kungiyar ta Turkiya a bazarar da ta gabata . (Guardian), external

Ita ma Leicester City ta na son ta dauko Zaha daga Galatasaray. (Athletic - subcription required), external

Arsenal a shirye take ta saka takunkumi kan barin dan wasan gaba na Ingila Eddie Nketiah mai shekara 25 daga kungiyar domin komawa Marseille a kan yuro miliyan 25 (Athletic - subscription required), external

Wolverhampton Wanderers na zawarcin dan wasan gefe na Ajax da Portugal Carlos Forbs dan shekara 20 a matsayin wanda zai maye gurbin Pedro Neto, mai shekara 24, wanda zai koma Chelsea. (Fabrizio Romano), external

West Ham United na gab da kulla yarjejeniya da dan wasa mai tsaron bayan Faransa Jean-Clair Todibo mai shekara 24 daga Nice yayin da take fuskantar gogaya daga Juventus. (Telegraph - subscription required), external

Kungiyar Queens Park Rangers na sha’awar dan wasan tsakiya na Japan Koki Saitp mai shekara 22 wanda yanzu ke taka leda a kungiyar Lommel ta kasar Belgium (West London Sport), external