Har yanzu Liverpool ta dage a kan Gordon,Real Madrid da PSG na zawarcin Acheampong.

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta dage a kan dan wasan gaban Ingila da Newcastle Anthony Gordon. Tattaunawar sayan dan wasan mai shekara 23 ta ruguje a watan yuni kuma watakila farashin Gordon ya karu. (Liverpool Echo), external
Kocin Aston Villa Unai Emery na son ya dauko dan wasan gaban Portugal Joao Felix, mai shekara 24 wanda ya kosa ya bar Atletico Madrid. (Birmingham Live), external
Real Madrid da Paris St-Germain na nazari a kan dan wasan bayan Chelsea Josh Acheampong, dan shekara 18, a matsayin wanda zai rike mu su baya ta gefe dama. Dan wasan Ingila ya kamala samun horo ne a kwalejin horas da ‘yan wasa ta Chelsea. (Independent), external
Ana sa ran za a yi wa dan wasan bayan West Ham Kurt Zouma gwajin lafiyarsa a Shabab Al Ahli bayan da suka kulla yarjejeniyar sayan dan wasan Faransaa mai shekara 29. (Sky Sports), external
Leicester na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiyar Argentina da Brighton Facundo Buonanotte dan shekara 19 domin a ba ta shi aro. (Mail), external
Real Sociedad na kokarin shawo kan dan wasan tsakiyar Sfaniya Martin Zubimendi mai shekara 25 wanda Liverpool ke zawarcinsa a kan ya yi watsi da tayin zuwa Anfield. Dan wasan zai iya tafiya ne kan fam miliyan 51. (Times - subscription required), external
Liverpool ta yi watsi da tayin da ake yi wa dan wasan bayan Netherlands Sepp van den Berg dan shekara 22. Hoffenheim da Stuttgart da Wolfsburg da Mainz da Borussia Monchengladbach da Bayer Leverkusen duk suna zawarcinsa . (Sky Germany), external
Brentford ta amince da yarjejeniyar bada aro wadda ta bada damar sayan dan wasan Sweden Jens Cajuste mai shekara 24 daga Napoli a kan fam miliyan 10. (Fabrizio Romano), external
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daraktan wasanni na Valencia Miguel Angel Corona ya ce Atletico Madrid ta yi kokarin soke yunkurin da suka yi na sayan dan wasan Chelsea dan kasar Ingila Conor Gallagher, mai shekara 24, domin ba da fifiko kan cinikin dan wasan tsakiyar kulob dinsa Javi Guerra, mai shekara 21. (Athletic - subscription required), external.
Birmingham City ta amince ta kulla yarjejeniya da Rennes kan yiwuwar sayan dan wasan Wales Jordan James, mai shekara 20. (Independent), external.
Marseille ta ci gaba da zawarcin dan wasa mai kai hari na Ingila da Arsenal Eddie Nketiah, mai shekara 25. (Sky Sports), external
Bournemouth na tattaunawa da Barcelona don siyan dan wasan bayan Mexico Julian Auraujo, mai shekara 22, kan kudi Yuro miliyan 10 (Fabrizio Romano), external
Fulham ta karfafa zawarcin da ta ke yi wa dan wasan bayan Aston Villa Diego Carlos. Ana sa ran dan kasar Brazil mai shekaru 31 zai tafi kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa kuma Villa ta nuna sha’awa . (Telegraph - subscription required), external











