Diego Maradona: Shahararren ɗan ƙwallon duniya ya mutu

Asalin hoton, Getty Images
Shahararren ɗan ƙwallon duniya Diego Maradona ya mutu yana da shekara 60.
Ya rasu ne ranar Laraba sakamakon bugun zuciya.
An yi nasarar yin tiyata a ƙwaƙwalwar tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar na Argentina kuma kocinta a farkon watan Nuwamba.
Daga nan ne aka sanar cewa za a yi masa magani kan jarabar shan barasa.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin shahararrun 'yan ƙwallon ƙafar duniya, Maradona shi ne kyaftin na Argentina lokacin da ta lashe Kofin Duniya a 1986, inda ya murza leda mai ƙayatarwa.
A saƙon da ta wallafa a shafin Twitter, hukumar ƙwallon ƙafar Argentina ta bayyana "matuƙar baƙin cikinta bisa mutuwar gwarzonmu", tana mai ƙara wa da cewa: "Za ka ci gaba kasancewa a zukatanmu."
Ɗan ƙwallon Argentina da Barcelona Lionel Messi ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Maradona, yana mai cewa shi "Mahadi ne mai dogon zamani".
"Wannan ranar matuƙar baƙin ciki ce ga dukkan 'yan ƙasar Argentina da masu son ƙwallon ƙafa," in ji Messi. "Ya bar mu amma yana raye saboda Diego Mahadi ne."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Maradona ya murza leda a ƙungiyar Barcelona da Napoli lokacin da yake kan ganiyarsa, inda ya lashe Kofunan Gasar Serie A da ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Italiya.
Ya zura ƙwallo 34 a wasanni 91 da ya murza wa Argentina, inda ya wakilci ƙasar a gasar cin Kofin Duniya sau huɗu.
Maradona ya jagoranci ƙasarsa a 1990 inda suka kai wasan ƙarshe a Italiya, ko da yake sun sha kashi a hannu Yammacin Jamus, amma ya sake jagorantarsu zuwa Amurka a 1994, sai dai an kore shi saboda samunsa da laifin shan ƙwayoyin ƙara kuzari.
Lokacin da ya komo karo na biyu domin sana'arsa ta ƙwallon ƙafa, Maradona ya sha fama da jarabar shan hodar ibilis kuma an haramta masa murza leda tsawon wata 15 bayan gwajin da aka yi masa a 1991 ya nuna cewa yana shan ƙwayoyi.












