Best Fifa Football Awards 2020: 'Yan Liverpool hudu na takarar gwarzon kwallon kafa na duniya

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Liverpool Virgil van Dijk da Mohammed Salah da Sadio Mane da kuma Thiago Alcantara na cikin jerin sunayen 'yan wasan Liverpool da ke takarar lashe kambun gwarzon dan wasan hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.
Shi ma dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin De Bruyne na daga cikin yan wasa 11 da aka rairaye don lashe kyautar.
A bangaren mata kuwa, 'yar wasan Ingila da Manchester City Lucy Bronze ta samu shiga jerin wadanda ke takarar lashe kambun.
Jurgen Klopp na Liverpool da Marcelo Bielsa na Leeds United sun samu shiga jerin masu horar da 'yan wasa mafi bajinta a bana.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce za a zabo gwarazan ne a kuri'ar da kyaftin da masu horar da kasashe a fadin duniya za su jefa.
Bugu da kari za a ba wakilan gidajen jarida sama da 200 damar jefa kuri'unsu ta yanar gizo.
Za a fara jefa kuri'ar ranar 25 ga watan Nuwamba har zuwa 9 ga watan Disamban 2020, kafin sanar da wadanda suka lashe kyautar a ranar 17 ga watan Disambar.
A wani bangaren, kwallon da dan wasan gaban Tottenham Son Heung-min ya ci Burnley na daga cikin kwallayen da ke takarar mafi kayatarwa da ake yi wa lakabi da 'Fifa's Puskas Award'.
A bangaren kwallon mata, yar kasar Scotland Caroline Weir, mai taka leda a Manchester City, na cikin jerin masu neman Fifa's Puskas Award din.
Ga jerin sunayen 'yan kwallo maza masu neman lashe 'Best Fifa Football Awards 2020'
Thiago Alcantara (Spain, Liverpool)
Cristiano Ronaldo (Portugal, Juventus)
Kevin de Bruyne (Belgium, Manchester City)
Robert Lewandowski (Poland, Bayern Munich)
Sadio Mane (Senegal, Liverpool)
Kylian Mbappe (France, Paris St-Germain)
Lionel Messi (Argentina, Barcelona)
Neymar (Brazil, Paris St-Germain)
Sergio Ramos (Spain, Real Madrid)
Mohamed Salah (Egypt, Liverpool)
Virgil van Dijk (Netherlands, Liverpool)
Ɓangaren mata
Lucy Bronze (England, Manchester City)
Delphine Cascarino (France, Lyon)
Caroline Graham Hansen (Norway, Barcelona)
Pernille Harder (Denmark, Chelsea)
Jennifer Hermoso (Spain, Barcelona)
Ji So-yun (South Korea, Chelsea)
Sam Kerr (Australia, Chelsea)
Saki Kumagai (Japan, Lyon)
Dzsenifer Marozsan (Germany, Lyon)
Vivianne Miedema (Netherlands, Arsenal)
Wendie Renard (France, Lyon)
Maza masu horarwa
Marcelo Bielsa (Argentina, Leeds United)
Hans-Dieter Flick (Germany, Bayern Munich)
Jurgen Klopp (Germany, Liverpool)
Julen Lopetegui (Spain, Sevilla)
Zinedine Zidane (France, Real Madrid)
Mata masu horarwa
Lluis Cortes (Spain, Barcelona)
Rita Guarino (Italy, Juventus)
Emma Hayes (England, Chelsea)
Stephan Lerch (Germany, Wolfsburg)
Hege Riise (Norway, LSK Kvinner)
Jean-Luc Vasseur (France, Lyon)
Sarina Wiegman (Netherlands, Dutch national team)











