Covid-19: Shugabanni mata sun fi maza yaƙar cutar korona a duniya - Bincike

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Mariana Sanches
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brazil
Shugabancin da mata ke bayarwa ya ja hankalin mutane matuka yayin wannan annobar, kuma akwai hujjar faruwar haka.
Tun da farko shugabannin kasashe kamar Jacinda Ardern ta New Zealand da Tsai Ing-wen ta Taiwan da Sheikh Hasina ta Bangladesh sun sha yabo saboda daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar korona da suka yi tun da wuri-wuri.
Amma ba a duba dangantakar da ke tsakanin kasancewa mace da kulawa da kiyaye lafiya ba - sai yanzu.
Wani sabon bincike a Brazil na cewa samun mace a matsayin shugaba na iya ceto rayuka masu yawa yayin da ake fama da annoba, idan aka kwatanta da samun namiji yana jagorantar kasa.
Masu binciken sun gano cewa garuruwan da mata ke jagoranta a cikin kasa na samun saukin kimanin kashi 43 cikin 100 na mace-macen da ake samu daga Covid-19, kuma nan samun raguwar kashi 30 cikin 100 na wadanda ake kwantarwa a asibitoci idan aka kwatanta da garuruwan da 'yan siyasa maza ke mulki.
Masu binciken sun ce sakamakon na iya zama haka ne domin suna daukan matakan kariya - kamar sanya takunkumi da hana tarurrukan jama'a - wanda mata sun fi karkata wajen daukarsu.
"Sakamakon binciken namu ya tabbatar da cewa shugabanni mata sun fi maza kokari wajen dakile matsalolin da su ka shafi yaduwar cututtuka."
Ceto rayuka

Asalin hoton, Getty Images
Masu binciken sun mayar da hankulansu ne kan mazaunin jama'a 5,500 na Brazil zuwa ga garuruwa 700 wadanda aka yi zabukan shekarar 2016 - wanda aka yi kunne doki tsakanin wata mata da wani namiji.
Sun kuma duba halin da ake ciki a garuruwan da mazauna cikinsu ba su wuce mutum 200,000 ba, kuma garuruwan sun kasance inda aka yi takara a zaɓe ɗaya kacal.
Bisa alkaluman hukuma, an gano cewa wuraren da mata ke jagoranta na samun raguwar kashi 43 cikin 100 na masu mutuwa daga Covid-19 idan aka katanta da wuraren da maza ke mulki.
Masu jinya kuma sun ragu da kimanin kashi 30 cikin 100.

Wannan daidai yake da ire-iren abubuwan da mata suka fi zaba yayin da suke bisa karagar mulki.
Kamar yadda binciken kuma ya nuna, mata sun fi maza daukan matakan kariya daga kamuwa daga cututtuka fiye da maza.
Masu binciken sun kuma ce idan da an bi tsarin da matan ke bi, da an sami raguwar mamata na kashi 15 cikin 100.
Ko kuma a ce, da mutum 75,000 da suka mutu - saboda annobar Covid-19 - da suna nan da ransu.
Bambance-bambance tsakanin mata da maza

Asalin hoton, Getty Images
Tamabaya a nan ita ce: Me yasa mata suka fi maza daukan matakai masu amfanin jama'a fiye da maza kamar yadda wannan binciken ya gano?
Masu binciken sun duba abubuwa masu yawa, kamar shekaru na haihuwa da yawan ilimin da wadanda aka bincika ke da shi, amma ba su gano wani abu mai alaka da su ba.
Wani abu kuma shi ne mata masu shugabanci sun fi daukan matakan hana walwala ko a cikin biranen da Shugana Jair Bolsonaro mai ra'ayin ƴan mazan jiya sun fi samun ƙuri'u a can.

Asalin hoton, EPA
Gagete-Miranda, wadda mai bincike ce a wata jami'a mai suna Università' degli Studi di Milano Bicocca a ƙasar Italiya ta ce halayyar mata ta neman kaucewa fadawa matsala na iya bayar da amsa ga masu son sanin dalilin da yasa su ke daukan matakan kariya fiye da maza.
"Dama akwai binciken da ke nuna cewa mata sun fi maza daukar matakan kariya wajen yakar annobar Covid-19, misali bayar da tazara da amfani da takunkumi", kamar yadda ta shaida wa BBC.
Ƙarfin mulki na siyasa

Masu bincike a jami'o'in Sao Paulo da na Barcelona, da kuma na Insper ne suka gudanar da binciken.
Wani bincike da aka wallafa a 2020 a mujallar "Journal of Applied Psychology" ta gano cewa jihohin Amurka da ke da gwamnoni mata ba su sami masu mutuwa masu yawa ba idan aka kwatanta su da wadanda maza ke mulki.
Wani binciken da aka wallafa a bana, wanda masu bincike daga jami'o'in Liverpool da na Reading suka yi, ya gano cewa kasashen da mata ke jagoranta sun fi samun ci gaba a fagen yaki da Covid-19 idan aka kwatanta da wadanda maza ke jagoranta.











