Wataƙila Crystal Palace ta sayar da Mateta, Napoli na son Mainoo

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Crystal Palace ta saurari tayin da za a yi wa Jean-Philippe Mateta a lokacin bazara idan ba ta iya sabunta yarjejeniya da dan wasan Faransa mai shekara 28 ba.(Sun)
Napoli na son ta dauki sabon dan wasan tsakiya a watan Janairu kuma hankalin kungiyar ta Serie A na kan dan wasan Manchester United mai shekara 20 dan kasar Ingila Kobbie Mainoo.Gazzetta dello Sport)
Brighton na iya komawa Cologne domin sayen dan kasar Jamus Said el Mala mai shekaru 19 a watan Janairu a kan yarjejeniyar da za ta kai Yuro miliyan 35 (Teamtalk)
Manchester United da Liverpool da Chelsea su ma suna son daukar El Mala, sai dai ana ganin United ce za ta iya samun galaba kan dan wasan (Talksport)
Fulham za ta biya AC Milan Yuro miliyan 28 don dan wasan Nijeriya, Samuel Chukwueze mai shekara 26 ya koma dan wasa na dindindin. (Calcio Mercato)
Manchester United da Arsenal da Real Madrid na zawarcin dan wasan Eintracht Frankfurt na Jamus Nathaniel Brown mai shekaru 22. (Bild - in German)
Tottenham da Newcastle da Aston Villa na iya zawarcin dan wasan Brentford dan kasar Brazil Igor Thiago mai shekaru 24 a watan Janairu (Caught Offside)
Dan wasan Mexico Santiago Gimenez zai iya barin AC Milan a watan Janairu inda West Ham da Sunderland suka nuna suna son daukar dan wasan mai shekaru 24.(Gazzetta dello Sport)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
West Ham ta sa ido sosai kan golan Wolves, mai shekara 32, dan Portugal, Jose Sa, kafin kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu (Football Insider)
Eintracht Frankfurt ta fasa daukan Niclas Fullkrug na West Ham a watan Janairu amma sauran kungiyoyin Bundesliga na ci gaba da zawarcin dan wasan na Jamus ciki har da Wolfsburg.(Florian Plettenberg)
Roma na zawarcin dan wasan gaban Tottenham dan kasar Faransa Mathys Tel, mai shekara 20, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24.(Ekrem Konur)
Newcastle na bibiyar dan wasan tsakiyar Morocco Bilal El Khannouss, mai shekara 24, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Stuttgart daga Leicester City.(Teamtalk)
Chelsea na da kwarin gwiwar kulla yarjejeniya da dan wasan Lille dan kasar Faransa Ayyoub Bouaddi mai shekaru 18 da kuma dan wasan Metz na Luxembourg mai shekaru 16 Brian Madjo.(Caught Offside)
Barcelona na kokarin sayen dan wasan Ingila JJ Gabriel mai shekara 15 daga Manchester United.(Sun)














