Kungiyoyin Saudiyya na zawarcin Salah, Liverpool ta sake tattaunawa da Guehi

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyi a gasar Saudiyya sun dage wajen son sayen dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 33, bayan da kocin Liverpool ya ki sa shi a cikin 'yan wasa a ranar Lahadi.(Talksport)
Liverpool ta sake tattaunawa da wakilan dan wasan Ingila Marc Guehi a yunkurin dauko dan wasan mai shekara 25 daga Crystal Palace a watan Janairu, bayan da ya kasa kulla yarjejeniya a bazara.(Teamtalk)
Manchester United na zawarcin dan wasan Olympiacos na Girka Christos Mouzakitis, yayin da Real Madrid kuma ke nazari kan tayin fam miliyan 25 kan dan wasan mai shekaru 18.(Mail)
Har yanzu Barcelona ba ta yanke shawarar sayen dan wasan Ingila, Marcus Rashford ba, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ba aronsa da Manchester United ta bayar ta zo karshe .(Sport)
Liverpool na cikin kungiyoyin da ke son daukar dan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25.(Football Insider)
Ita ma Tottenham ta kara kaimi a zawarcin da take yi wa Semenyo kuma za su iya tattaunawa da dan kasar Ghana a watan Janairu.(Sky Sports)
Gary O'Neil na cikin wadanda za su iya maye gurbin kocin Leeds idan sun yanke shawarar korar kocin dan Jamus Daniel Farke (Football Insider)
West Ham da Brentford na tunanin zawarcin dan wasan Portugal, Tiago Gabriel, mai shekara 20 a watan Janairu, amma suna fuskantar hamayya daga Juventus kan dan wasan na Lecce.(The i Paper)
Dan wasan baya Timothy Castagne, mai shekara 29, zai iya barin Fulham a watan Janairu domin tabbatar da kasancewarsa a cikin tawagar Belgium a gasar cin Kofin Duniya ta bazara mai zuwa.(DH - in French)
Golan Italiya Guglielmo Vicario na son ya bar Tottenham inda Inter Milan ta nuna sha'awar daukar dan wasan mai shekara 29.(La Gazzetta dello Sport)
Liverpool da Arsenal na shirin sayen dan wasan Real Madrid dan kasar Brazil Rodrygo mai shekara 24 a watan Janairu.(Caught Offside)
Liverpool ta sha gaban Barcelona a yunkurin dauko dan wasan Brazil Ederson mai shekara 26 daga Atalanta. (Fichajes )
Bayern Munich na son ta zauna kan teburin shawara don sayar da Sacha Boey dan Faransa mai shekara 25 kan Yuro miliyan 15 ko fiye da haka wanda Crystal Palace ke zawarcinsa. (Bild)
Kungiyoyin Firimiya da dama na bibiyar golan Benfica dan kasar Ukraine Anatoliy Trubin, mai shekara 24 (GiveMeSport)














