Trafford na son barin Man City, AC Milan na harin Jean-Philippe Mateta

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar Manchester City James Trafford mai shekaru 23, na duba yiwuwar barin ƙungiyar a watan Janeru, bayan da ya ƙi karɓar umarni, sakamakon zuwan Gianluigi Donnarumma daga Paris St-Germain, yayin da mai tsaron ragar Jamus, Stefan Ortega, mai shekaru 33, shi ma na duba yiwuwar sauya ƙungiya. (Mail)
Ɗan wasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta mai shekaru 28, na son komawa taka leda Serie A, musamman ma AC Milan. (Talksport)
Atletico Madrid ta yi watsi da tayin Manchester United Conor Gallagher da zai a matsayin ɗan wasan aro a kakar wasan da ya bata, sai dai ƙungiyar Spaniya za ta iya ɗaukar ɗan wasan ƙasar Ingilar mai shekaru 25, kan fam miliyan 26, a watan Janerun ko a kakar siyar da ƴan wasa. (Here We Go Podcast with Fabrizio Romano)
Har yanzu Eintracht Frankfurt na son ɗaukar ɗan wasan Newcastle William Osula, mai shekaru 22, yayin da Eintracht Frankfurt si suka ce sun fasa ɗauko ɗan wasan West Ham Niclas Fullkrug mai shekaru 32. (Sky Sports Germany - in German)
Arsenal ta amince da ɗaukar ƴan biyu kuma yan Ecuador Edwinda da Holger Quintero, masu shekaru 16, daga Independiente Del Valle bayan sun cika shekaru 18 a ranar 18 ga watan Agusta, 2027. (ESPN)
Sunderland na son ɗauko ɗan wasan Arsenal Matteo Guendouzi mai shekaru 26, yayin da ɗan wasan Lazio ke son komawa ƙungiyar ta BlackCa. (i Paper - subscription required)
Roma na duba yiwuwar ɗuko dan wasan Tottenham mai shekaru 20 Mathys Tel a wata Janeru, idan har suka gaza ɗauko ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee. (Il Messaggero - in Italian)
Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Eintracht Frankfurt kan ɗauko dan wasan ƙungiyar Nathaniel Brown, wand ake da sha'awar taka leda a Real Madris da Barcelona. (Florian Plettenberg)
Tottenham na son ɗauko ɗan wasan Porto Samu Aghehowa mai shekaru 21, a watan Janeru, sai dai sun ce za su iya fasa siyen sa idan har Manchester City a yuƙunrin d auke ci na ɗauko ɗan wasan Bournemouth Antoine Semenyo. (Teamtalk)
Tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos na son komawa truai, idan kwantaraginsa ta ƙare da Monterrey, a ƙarshen Disambar nan, yayin da AC Milan ke cikin jerin ƙungiyoyin da ke son ɗaukarsa. (Calciomercato - in Italian)
Nottingham Forest na ci gaba da sa ido kan dan wasan Inter Milan Stefan de Vrij mai shekaru 33, bayan da idan kwantaraginsa zai ƙare a kakar wasanni. (Football Insider)











