Manchester City za ta ɗauki aron Joao Felix, Chelsea na zawarcin Mec

Joao Felix

Asalin hoton, EPA

Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle ta kusa kammala cinikin ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 24, Marc Guehi, daga Crystal Palace a kan £60m. (Telegraph - subscription required)

Manchester United ta ci gaba da neman ɗan wasan tsakiya bayan fuskantar koma baya a shirin ta na ɗaukar Manuel Ugarte mai shekara 23 daga PSG. (Athletic - subscription required)

Atletico Madrid ta yi tayin bayar da ɗan wasan gaban Portugal mai shekara 24, Joao Felix ga Manchester City a matsayin aro, daga cikin yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaban Argentina, Julian Alvarez. (Mail)

West Ham ta samu tangarɗa a ƙoƙarin ta na ɗaukar ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 26 bayan da ya nuna sha'awar sa ta komawa taka leda a Manchester United. (Sun)

Fatar Liverpool ta ɗaukar ɗan wasan bayan Juventus mai shekara 27, Gleison Bremer ta rushe bayan ɗan wasan Brazil din ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar ta Italiya. (Fabrizio Romano)

Amma Liverpool ta ƙara samun ƙarfin gwiwa a ƙoƙarin ta na ɗaukar ɗan wasan gaban Juventus mai shekara 26, Federico Chiesa, bayan ta cika dukkan sharudɗa da ake buƙata. (Mirror)

Chelsea na tattaunawa da Atletico Madrid kan cinikin ɗan wasan gaban Sifaniya mai shekara 20, Samu Omorodion a kan £35m (Sky Sports)

Haka nan kuma Chelsea ta amince ta biya £20.5m domin daukar ɗan wasan tsakiyar Brazil mai shekara 16, Gabriel Mac daga Gremio. (Globo)

Fulham na ci gaba da tuntuɓar Manchester United kan cinikin ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 27, Scott McTominay. (Sky Sports)

Leicester City ce kan gaba a zawarcin ɗan wasan gaban Ivory Coast mai shekara 2, David Datro Fofana, daga Chelsea. (Fabrizio Romano)

Leeds United ta shirya gabatar da tayin £7m kan ɗan wasan gefen Norwich mai shekara 21, kuma ɗan ƙasar Ingila, Jonathan Rowe. (Telegraph)