Gallagher zai koma Atletico Madrid daga Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Chelsea, Conor Gallagher ya amince zai koma Atletico Madrid da taka leda.
Chelsea ta amince da tayin fan miliyan 33 daga ƙungiyar Sifaniya a makon da ya gabata, wanda tun farko ake fargabar watakila ɗan wasan Ingila ba zai amince da zuwa can ba.
Amma a daren Lahadi, sai Gallagher, mai shekara 24, ya shaida wa jami’an Atletico cewa ya yi farin ciki da tayin da aka yi masa, kuma a shirye yake ya koma buga La Liga.
A yanzu dai ana sa ran ɗan wasan na Ingila zai je Sifaniya domin auna koshin lafiyarsa, sannan ya saka hannu kan kwantiragi.
Hakan zai kawo karshen kaka 18 da Gallagher ya yi a Stamford Bridge.
Chelsea ta gabatar da ƙunshin ƙwantiragin kaka biyu da cewar za a kara masa wata 12, sai dai Gallagher bai amince ba, sakamakon rashin fayyace masa rawar da zai ke takawa.
An samu rarrabuwar kawuna tsakanin Gallagher da Chelsea, saboda an yi imanin bai dace da salon wasan koci Enzo Maresca ba, kuma ba za ake amfani da shi ba a fili koda yaushe.
Gallagher, wanda ya buga wasa biyar a gasar Euro 2024 da aka yi a Jamus, yana da sauran yarjejeniyar kaka daya da ta rage da Chelsea.
Chelsea ta gwammace ta sayar da Gallagher a wata kasar, maimakon ga abokan hamayya a Ingila, don haka ta bai wa Atletico damar cimma yarjejeniyar da ɗan wasan.











