Yadda kisan Ali Khamenei zai shafi ƴan Shi'a a Najeriya
Asalin hoton, JNIM
Har yanzu duniya na ci gaba da alhinin kisan jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran.
Ayatollah mai shekara 86 na da matuƙar tasiri a Iran da ma ƙasashen duniya, musamman tsakanin mabiya aƙidar Shi'a a faɗin duniya
Tuni dai mabiya ƙungiyar ƴan'uwa Musulmi a Najeriya ta ,yan Shi'a suka shiga jimaminsa ta hanayr gudanar da taron muzaharori da zanga-zangar lumana domin bayyana alhininsu.
Malam Sidi Mannir Mainasara ɗaya daga cikin manyan almajiran Sheikh Alzakzaky kuma wanda ya san rayuwar Ayatoullah Ali Khamenei, ya bayyana wa BBC yadda mabiya shi'a a faɗin duniya suka ji da rashinsa.
Ya ce kisan Ayatollah ya ƙara fito da martaba da tasirin aƙidar Shi'a ke da shi a Najeriya.
''Za ka sha mamaki idan ka ga yadda mutane suka ajiye bambancin aƙida suka riƙa yi mana ta'aziyyar rasuwarsa'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa abin ya ba su mamaki, yadda mutuwarsa ta mantar da al'umma bambancin aƙida.
'Ya taka irin rawar Khomeini'
Malam Sidi Mannir Mainasara ya ce tun bayan da ka naɗa Ayatollah Ali Khamenei matsayin jagoran addinin Iran ya yi ƙoƙarin ganin ya taka irin rawar da mutumin da ya gada ya ɗora ƙasar a kai.
''Daga shekarar 1989, lokacin da ya zama jagoran addinin Iran, bai taɓa sauka daga turbar da Imam Khomeini ya ɗora Iran a kai ba''.
Ya ce duk da cewa suna jin alhinin rashinsa, amma idan suka tuna cewa ya yi shahada sukan ji sanyi a ransu.
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wane giɓi Ayatollah ya bari?
Malam Sidi ya ce jagoran addinin ya bar babban giɓi a duniyar musulunci, musamman tsakanin mabiya aƙidar Shi'a.
''Mutuwarsa ta nuna cewa shi jagora ne na duniya da na wata ƙasa kaɗai ba'', in ji shi.
Ya ce bayan mutuwarsa duk musulmin duniya sun ankara tare da nuna damuwarsu game da rasuwar tasa.
''Ya tsaya wa al'ummar Falasdinawa raunana tsawon shekaru, kusan duka rayuwarsa ta tafi a wannan gwagwarmaya'', in ji shi.
Mutuwarsa za ta kawo wa Iran rauni?
Wasu mutane dai na ganin kisan jagoran addinin zai kawo rauni ga ƙasar Iran, wadda ba ta ga maciji da ƙasashen Yamma.
To amma Malam Sidi ya ce sam ba haka ba ne, sai dai ma abin da ya ƙaru.
''Mutuwarsa ba za ta tyaɓa zama rauni ga Iran ba, hasalima ƙarfafa gwiwar ƙasar ta yi'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa tun bayan mutuwarsa, zukatan al'ummar musulmai sun zafafa tare da ƙara ƙaimi.
''Indai Amurka tana tunanin kashe shi zai ƙara mata farin jini to akasin haka za ta samu'', in ji shi.
Ya kuma gargaɗi ƙawayen amurka musamman a gabas ta tsakiya da su yi taka tsantsan da ƙawancen.
''Dalili shi ne ita fa Amurka ba ta da aboki na dindindin'', in ji shi.
Zanga-zangar alhinin kisan
Asalin hoton, JNIM
Mabiyar aƙidar Shi'ar a Najeriya sun kuma gudanar da zanga-zangar lumana a wasu jihohin ƙasar, ciki har da Legas, da ke kudu maso yammacin kasar, domin nuna alhininsu kan kisan jagoran addinin na Iran.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun ratsa wasu sassan yankin Maryland, ɗauke da alluna da tutoci, suna allawadai da abin da suka kira mamaye Iran da kuma kisan gilla kan jagoranta wanda ya daɗe yana mulki.
An kashe Ayatollah Ali Khamenei ne a safiyar Asabar 28 ga Fabrairu a hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai tare da wasu manyan jami'an gwamnatin Iran.
Sauran wuraren da mabiya Shi'ar suka gudanar da zanga-zangar a Najeriyar sun haɗa da Kano da Yobe da Gombe da Bauchi a ranar Lahadi.
Shi'a a Najeriya
Shi'a, wadda aƙida ce da aka samu daga wasu mabiya addinin Musulunci ta yi ƙarfi ne a Najeriya bayan juyin juya halin ƙasar Iran, wanda ya sanya Ayatollah Khomeini ya zama jagoran addinin ƙasar a 1979.
Khomeini ya kasance abin koyi ga mabiya shi'a a Najeriya, inda suke yabon shi, kuma a wakokin da sukan rera suna nuna biyayyar su gare shi, sai kuma jagoransu na Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky.
An yi ƙiyasin cewa yawan mabiya aƙidar shi'a a Najeriya ya kai kimanin kashi biyar zuwa 17 na al'ummar Musulmin ƙasar.
Sai dai mabiya aƙidar sun sha karawa da hukumomi sanadiyyar gangami da tattaki da suke yi a kai a kai kan hanyoyin ƙasar.
A watan Disamban 2015 mabiya aƙidar sun yi wata mummunar arangama da sojojin Najeriya a birnin Zariya da ke jihar Kaduna, arewa maso yammacin ƙasar.
Lamarin, wanda ya janyo zazzafar muhawara, ana zargin cewa ya haifar da rasa rayukan ɗaruruwan mabiya aƙidar.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai