Yadda yaƙin Tigray ya ɗaiɗaita Mekelle babban birnin yankin

Asalin hoton, OTHERS

Yayin da yakin da ake yi a yankin Tigray na kasar Ethiopia ke kara tsanani, fararen hula na kara samun kansu a cikin rikici.

Kwamandojin kungiyar fafutikar neman 'yancin Tigray sun shiga daukar sabbin mayaka, inda tun a baya aka zarge su da tilasta wa mutane shiga yakin.

Haka su ma hukumomin kasar Eritrea, ana yi musu wannan zargin kasancewar sun shiga yakin ta bangaren mara baya ga Ethiopia.

BBC ta samu wani rahoto na musamman daga wani dan jarida da ke aiki a babban birnin yankin Tigray, Mekelle kan yadda jama'a ke rayuwa a wannan lokaci da ake yaki.

Kusan a kullum jirage marasa matuka na shawagi a saman babban birnin Mekelle, wanda ke da yawan al'umma kusan 300,000. Ina iya jin shawagin daya daga cikinsu a yayin da nake rubuta wannan makalar. Hakan ya sa ina jin babu tsaro.

A makonnin da suka gabata an yi luguden wuta a wuraren wasan yara da kuma yankunan da ke da gidajen kwana - babu tabbaci game da inda aka nufi kai hare-haren.

A wannan makon dakarun Tigray sun yi kira ga duk wanda yake ganin zai iya shiga yakin, wanda aka kwashe watanni 23 ana gwabzawa, kuma bisa ga alamu mutane na amsa wannan kira.

Wani mazaunin yankin, wanda BBC ta boye sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce ''Ana daukar duk wanda ya ki shiga aikin soji a matsayin wanda ya aikata wani mummunan sabo''.

Mafi yawan al'umar Tigray sun kafe cewa ba za su yi biyayya ga dokokin Habasha ba, a yayin da Firaiminista Abiy Ahmed ya zargi shugabannin yankin da son ballewa domin kafa kasarsu.

Kowa a nan na son kare 'yancinsu. Rikicin baya-bayan nan ya barke a karshen watan Agusta bayan tsayar da ayyukan jinkai da aka kwashe wata biyar ana gudanarwa a yankin.

Mutane daga kowanne bangare, ciki har da mata na kananan yara a shirye suke su shiga aikin soji domin kare kasarsu.

Daga ciki akwai wata matashiya mai shekara 23 wadda ta shaida mana cewa tana "alfahari da kasancewa 'yar Tigray, kuma ina farin ciki da horaswar da aka ba ni domin kare 'yanci na da kasata."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yankin Tigray na karkashin mamaya tun shekarar 2021, sannan kuma rayuwa a yankin na ci gaba da kasancewa cikin tasku.

A halin yanzu fiye da shekarar guda kenan tun bayan da aka katse layukan waya da na intanet, inda aka hana mu hulda da sauran yankunan duniya.

Mutane sun koma amfani da wasika domin sadarwa tsakanin iyalai da abokai, ko kuma su je yankin Amhara da ke kan iyaka da Habasha domin samun damar yin kiran waya da cirar kudi da 'yan uwansu da ke kasashen waje ke aika musu.

Mutane da yawa kan taru a gefen titi domin sauraron akwatin rediyo guda daya, domin sanin halin da duniya ke ciki.

Kowa na magana kan yadda za a samu zaman lafiya, kuma suna bin matakan da suka dace domin samun zaman lafiya, to amma da yawa sun yi amanna cewa gwamnatin Habasha ba ta shirya wa tataunawar zaman lafiya ba, saboda ba su daina kai hare-haren boma-bomai ba.

Mutane ba sa iya tura kudi, ko cirarsu a bankuna ba, saboda bankunan a rufe suke, dan haka babu wasu harkokin kasuwanci da ke gudana.

Wannan dalili ne ya haddasa bude kasuwannin gefen titi, wadanda a baya kafin yakin, doka ba ta amince da su ba, da kasuwannin musayar kudi na bayan fage da ke tatsar kwastomomi kashi 30 zuwa 50 cikin 100.

Makwabtana na rayuwa da kudaden da 'yan uwansu ke aiko musu daga Amurka da Canada. Daya daga cikinsu ya shaida min cewa ba zai iya ciyar da 'ya'yansa biyar ba, muddin 'yan uwan ba su aiko masa kudi ba, yana da 'yan uwa biyu a Amurka, kuma sau hudu suna aiko masa da kudi tun bayan fara mamayar.

Rikicin ya hana shigar da muhimman ababen more rayuwa cikin yankin, wadanda suka hada da man fetur, abin da ya sa mutane da dama ke yin tafiye-tafiyensu a kafa, inda wasu kuma suka koma hawa jakuna.

Bayanan hoto, An toshe birnin Mekelle ta yadda mutane ba za su iya mu'amala da sauran jama'ar duniya ba

Farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa. Alal misali alkamar da muke amfani da ita wajen yin Biredi da sauran abincin gargajiya da muke ci yau-da-kullum, na kara hauhawa a kowanne mako. A halin yanzu farashin buhun alkama mai nauyin kilogiram 100, ya kai dala 265, a maimakon dala 85 da ake sayar da ita a shekarar da ta gabata.

Mutane na mutuwa sakamakon karancin magunguna, wadanda ake da su farashinsu ya yi tashin gwauron zabo.

A yayin da sabbin hare-hare ta sama ke ci gaba da kashe fararen hula, ana ci gaba da tilasta wa kananan yara shiga aikin soji.

Wata mata mai shekara 29, ta shaida min cewa uku daga cikin 'yan uwanta - maza biyu da mace daya - yanzu sun shiga aikin soji.

Watanni biyu da suka gabata takan yi amfani da 'yan kudadenta, domin girka abinci ga mayakan da ke filin daga.

Mutane kan taimaki makwabtansu - wadanda 'yan uwansu ke filin daga - da abincin da za su ci.

Al'umar yankin sun shiga murna da farin ciki a makon da ya gabata lokacin da suka samu labarin cewa kungiyar kasashen Afirka za ta jagoranci tattaunawar sulhu a Afirka ta kudu.

To sai dai ba a samu nasarar yin tattaunawar ba, sakamakon wasu dalilsai da ba abayyana ba.

Al'uma da dama na cike da bukatar samun zaman lafiya a yankin, inda masallatai da majami'u ke cika cikin dare domin addau'ar kawo karshen wannan yaki.

BBC ta boye sunan dan jarida da kuma mutanen da ya yi hira da su saboda dalilai na tsaron lafiyarsu.