Sarauniyar kyau da ta sayar da rai don yin tafiya mai cike da hatsari zuwa Birtaniya

.

Asalin hoton, SELAMAWIT TEKLAY

Fitacciyar Sarauniyar kyau ta ƙasar Habasha, Selamawit Teklay, wacce ta fito daga yankin Tingray da yaƙi ya ɗaiɗaita, ta bayyana yadda ta jefa kanta cikin hatsarin tafiya cikin teku domin neman mafaka a Birtaniya.

Da fari Sarauniya Selamawit ta je ƙasar Faransa amma daga bisani ta sanya rayuwarta cikin hatsarin tafiya mai nisa cikin ƙaramin kwale-kwale tare 'yan uwanta 'yan ci-rani.

Yankin Tigray ya faɗa cikin yaƙin basasa a ƙarshen shekarar 2020, abin da ya yi sanadiyyar kisan fararen hula masu ɗimbin yawa, da yawaitar fyaɗe tare kuma da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira 'tsananin ƙangin yunwa' saboda wahalar abinci.

Ta bayyana wa BBC yadda ita da sauran 'yan uwanta 'yan ci-rani suka yi wannan tafiya, duk kuwa da sanin irin hatsarin da ke tattare da ita.

"Na sha matuƙar azaba kafin na isa Birtaniya. Na ga 'yan uwana 'yan Tigray da yawa da suka faɗa cikin teku. Da kyar na tsallake rijiya da baya," in ji ta.

Ta kara da cewa: "Ba zan taɓa mantawa da abin da ya faru a watan Nuwamban 2021 ba.

Mun shafe makonni biyu muna kwana a dazukan Calais da ke ƙasar Faransa. Ga tsananin sanyi, ba abincin da za mu yi kalaci da shi, babu ruwan da za mu jiƙa maƙogoronmu, mun sha azaba marar misaltuwa.

Sai da muka jira 'yan sumoga suka zo muka tsadance da su, suka bi da mu ta ɓarauniyar hanya.

Sukan kwashi 'yan ci-rani cikin talatainin dare domin kauce wa haɗuwa da 'yan- sanda."

.

Asalin hoton, AFP

Ta ce: "Jirgin farko da ya fara tashi cike da 'yan uwana ya nutse a teku lokacin da yake ƙoƙarin tsallakawa, amma cikin ikon Allah masu gadin tekun sun kubutar da su.

Muna jiran kwale-kwale ya zo ya kwashe mu, sai muka samu wannan mummunan labari, mun girgiza matuƙa, to amma ba mu da zaɓi, dole mu yi wannan tafiya.

Cikin 'yan kwanaki kuwa wani ɗan ƙaramin kwale-kwale ya ɗauke mu, muka tafi, tafiya ce mai cike da hatsari ga tsananin sanyin teku."

Sarauniyar kyawun ta kara da cewa: "Muka ɗau harama zuwa Birtaniya, domin tseratar da rayukanmu. To amma tafiyar tamu ba iya lalube cikin duhu kadai ba ne, tafiya ce ta rai kwakwai-mutu kwakwai.

Muna cikin tafiya kwatsam! sai injin jirginmu ya faɗa cikin teku, nan take wani Balarabe ya yi tsalle cikin ruwan domin lalubo shi, sai wani ɗan uwanmu ɗan Tigray shi ma ya fada ruwan domin taimaka masa.

.

Asalin hoton, AFP

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To amma sai ya nutse, mun yi ta nemansa, mun jiyo ihunsa, amma ba mu iya ganinsa ba."

Ta ce daga nan "muka yi ta neman taimakon masu gadin teku, amma sai bayan sa'o'i uku suka zo, sai dai kash! ƙaddara ta riga fata, domin kuwa ya mutu, a gaban idona aka tsamo gawarsa.

To amma shi Balaraben ya yi sa'a bai mutu ba, ya samu nasarar kubuta, lallai na yi da-na-sanin fara wannan tafiya.

Bayan mun isa Birtaniya da kwana hudu, muka samu labarin cewa kwale-kwalen da ya ɗauko sauran 'yan uwanmu ya nutse da fasinjojin da ke cikinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ilahirin mutanen da ke cikinsa.

Mutum biyu daga ciki manyan ƙawaye na ne, ɗayar ma tare muka taso tun muna yara a garinmu Mekelle. Na tausaya wa kaina, na tausaya wa mutanena, na kuma ji raɗaɗin rabuwa da iyayena.

Iyayena ba su san cewa zan zo ƙasar nan ta wannan hanya ba, a lokacin da na fara wannan tafiya, na fada wa kaina cewa komai wahalar tafiyar ba za ta kai tsananin da muke ciki a yankin Tigray ba. Lallai mun ga tashin hankali a gida."

.

Asalin hoton, AFP

Amma kuma lallai wahalar da ke cikin tafiyar tamu, wahala ce da babu mai hankalin da zai yi tunanin tunkarta. Ban taɓa tunanin cewa zan bar ƙasata ba, ba ni ma da sha'awar hakan kwata-kwata.

A baya a duk lokacin da na bar ƙasarmu game da sabogogina na sarautar kyau, ko wasu aikace-aikacen, nakan koma gida. Ina da sana'ar da nake gudanarwa garinmu Mekelle, wato sayar da tufafin zamani.

A lokacin kasuwanci na tsaka da haɓaka a Mekelle, ina jin daɗina, kawai sai aka fara yaƙin basasa a watan Nuwamban 2020, yaƙin da ya yi sanadiyyar dubban rayuka.

Yaƙin ya haifar da tsananin yunwa, da yawaitar fyade, da wasu abubuwan da baki ma ba zai iya furtasu ba, an kulle asusun ajiya na Bankunanmu, babu wanda zai iya cire kuɗinsa .

.

Asalin hoton, SELAMAWIT TEKLAY

An cutar da iyalaina da dama, amma kuma na yi sa'a ba a yi min fyade ba kamar sauran 'yan uwana, amma kuma an raunata min tunanina.

An yi ruwan boma-bomai a Mekelle, an tilasta mana barin gidajenmu, inda muka koma ƙauye

Daga nan ne kuma na fara tunanin barin ƙasarmu, fatana shi ne samun zaman lafiya, saboda na yi imanin cewa zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.

Ni kaɗai ce 'ya a wajen iyayena, ina tuna irin shaƙuwa da ƙaunar da iyayena ke nuna min, musamman mahaifiyata.

Lokacin da na fara shiga sabgogin sarautar kyau, iyayena sukan ce na maida hankali wajen karatu na. To amma muradina na zama sarauniyar kyau ya hana ni cika wa iyayena burinsu.

Saboda tun ina da shekara 16 na fara takarar sarauniyar kyau ta garin Mekelle, gasa ce mai matukar burgewa.

Da na ƙara girma na shiga babbar gasar ta ƙasa a shekarar 2015 na kuma yi nasara.

Ban tsaya iya nan ba, a shekarar 2017 na shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya, inda 'yan takara 77 daga ƙasashe daban-daban na duniya muka fafata a gasar da aka gudanar a ƙasar Vietnam.

Kuma wannan shi ne karo na farko da na wakilci ƙasarmu a gasar saruniyar kyau ta duniya.

Na samu kyaututtuka masu tarin yawa, waɗanda suka buɗe min sabbin ƙofofin samun tallace-tallacen manyan kamfanoni da dama a faɗin duniya.

A shekarar 2018 ma, na sake shiga wata gasar ta duniya da aka gudanar a Koriya ta Kudu, sannan a shekarar 2019 ma na halarci gasar da aka gudanar a China.

.

Asalin hoton, Selamawit Teklay

To amma yanzu duka waɗannan sun zama tarihi, wai yanzu ni ce ke neman mafaka a Burtaniya.

Da fari sun sauke mu a Otal, yanzu kuma sun kai mu wani gida inda muke sayen abinci da kudinmu.

A baya-bayan nan dai gwamnatin Burtaniya ta shirya mayar da masu neman mafaka a kasar zuwa Rwanda. matakin da masu neman mafakar ba sa maraba da shi.