Akwai yiwuwar Salah ya koma Saudiyya da taka leda, Madrid da Man U na zawarcin Mouzakitis

Mohammed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Salah
Lokacin karatu: Minti 2

Gasar kwararu ta Saudiyya har yanzu tana da damar da za ta bayar da kudade don sayen dan wasan Masar, Mohammed Salah mai shekara 33 idan ya yanke shawarar barin Liverpool. (Telegraph)

Kungiyar Galatasaray ta Turkiyya na shirin yi wa Salah tayin kwantiragin fam miliyan 15 zuwa miliyan 16.5 a kowace kakar wasa.(Fichajes)

Real Madrid za ta fafata da Manchester United wajan daukar dan wasan Olympiakos da Girka Christos Mouzakitis, mai shekara 18. (Sun)

Watakila Tottenham ta sayi dan wasan Brighton da NetherlandsJan Paul van Hecke, mai shekara 25 a kan fam miliyan 40 . (Teamtalk)

Dan wasan Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, ya fada wa Crystal Palace cewa yana son ya bar kungiyar a watan Janairu mai zuwa.(Teamtalk)

Leeds na son daukan dan wasan AC Milan da Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 24, a watan Janairu (Fichajes)

Wolves za ta kyale dan wasan Sifaniya, Fer Lopez mai shekara 21 ya bar kungiyar a matsayin aro a watan Janairu bayan ya samu takaitaccen lokacin wasa.(Fabrizio Romano)

Brighton na bibiyar dan wasan Aston Villa da Netherlands Lamare Bogarde mai shekara 21.(Telegraph)

Newcastle na zawarcin dan wasan Palmeiras da Brazil Allan Elias mai shekara 21. (Goal)

Ita ma Arsenal na zawarcin dan wasan Elche da Sifaniya Rodrigo Mendoza mai shekara 21. (Sky Sports)

Chelsea na kokarin kulla yarjejeniya da dan wasan SF Cascades da kuma Burkina Faso Mohamed Zongo, mai shekara 16, duk da cewa tana fuskantar hamayya daga Manchester City da Manchester United (Mail)