PSG da Real na zawarcin Konate, Man City za ta sayar da 'yan wasa uku

Ibrahima Konate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ibrahima Konate
Lokacin karatu: Minti 2

West Ham ta saka dan wasan gaban Amurka da Norwich Josh Sargent, mai shekara 25, a jerin 'yan wasan da take son ta saya a watan Janairu.(Sun)

Manchester City ta shirya sayar da dan wasan gaban Brazil Savinho, mai shekara 21, da dan wasan baya na Ingila Rico Lewis, mai shekara 21, da kuma dan wasan Norway Oscar Bobb, mai shekara 22, a watan Janairu don samun kudin shiga kasuwar musayar 'yan wasa.Football Insider)

Paris St-Germain da Real Madrid na zawarcin dan wasan baya na Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26. (Caught Offside)

Ita ma Real Madrid na son dan wasan Portugal da Manchester United Diogo Dalot mai shekara 26. (Teamtalk)

Inter Milan na neman wanda zai maye gurbin golan Switzerland Yann Sommer mai shekara 36 a bazara mai zuwa kuma golan Tottenham da Italiya, Guglielmo Vicario mai shekara 26 shi ne kan gaba a cikin wadanda take nema. (Gazzetta dello Sport)

Tottenham na neman hanzarta tattaunawa kan sabunta kwantaragin dan wasan Sifaniya Pedro Porro, mai shekara 26, a yayin da Manchester City ke zawarcinsa.(Teamtalk)

Newcastle za ta fuskanci hamayya daga Tottenham da Aston Villa wajen sayen golan Manchester City dan kasar Ingila James Trafford, mai shekara 23.(Football Insider)

Watakila dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 31 ya bar Chelsea yayin da Leeds da Crystal Palace ke zawarcinsa . (Caught Offside)

AC Milan na zawarcin dan wasan West Ham dan kasar Jamus Niclas Fullkrug, mai shekara 32, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasanta mai kai hari na Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, saboda rashin amincewa da yadda Manchester United ke son ta tsara yarjejeniya. (Gazzetta dello Sport )

Sai Sunderland ta yi da gaske wajen ganin dan wasan tsakiya na Jamhuriyar Dimokuraddiyar Kongo Noah Sadiki mai shekara 20 ya ci gaba da tamaula a kungiyar saboda yana cikin 'yan wasan da suka dau hankalin Manchester United (Teamtalk)