Man United na zawarcin Ramos Sunderland na son Guendouzi

Asalin hoton, Getty Images
United na zawarcin tsohon dan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar kungiyar Monterrey ta Mexico.(Fichajes)
West Ham na bibiyar dan wasan Rio Ave dan kasar Brazil, Clayton, mai shekara 26, wanda ke kan gaba wajen zura kwallaye a gasar Firimiya ta Portugal. (Teamtalk)
Roma ta fara tattaunawa a hukumance kan sayen dan wasan Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, daga Manchester United a matsayin aro kan fam miliyan 30.(Gazzetta dello Sport)
Ita ma Sunderland na zawarcin tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Matteo Guendouzi, a kan fam miliyan 21.4 mai shekara 26, wanda ke taka leda a Lazio.(Sunderland Echo)
Kwantiragin dan wasan Faransa Ibrahima Konate zai kare a bazara mai zuwa amma dan wasan mai shekaru 26 na iya sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da Liverpool a makonni masu zuwa.(Football Insider)
Tsohon dan wasan Ingila da Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 32, yana son ya koma gasar Firimiya a watan Janairu, bayan da ya bar Besiktas a watan Agusta.(Athletic - subscription required)
Abu ne mai wuya dan wasan Ingila Ivan Toney, mai shekara 29, ya bar Al-Ahli a watan Janairu domin komawa gasar Firimiya saboda dalilan haraji. (Talksport)
West Ham na shirin zawarcin dan wasan Zulte Waregem, dan Najeriya Tochukwu Nnadi mai shekara 22 a watan Janairu.(Teamtalk)
Wolves na sha'awar sayen dan wasan Fulham Adama Traore, mai shekara 29 a watan Janairu, wanda ya shafe shekaru biyar a Molineux.(Football Insider)
Sheffield Wednesday na son dan wasan Manchester United Harry Amass da aka ba ta shi aro mai shekara 18, ya ci gaba da taka leda a wurinta har karshen kakar wasa ta bana duk da cewa ta rasa maki a gasar Zakarun Turai.(Sun)
Chelsea ta samu galaba kan Manchester City da Manchester United wajen daukar dan wasan SF Cascades da Burkina Faso Mohamed Zongo, mai shekara 16. (Mail)











