Arsenal na son Rodrygo, Bayern na shirin ganawa da Guehi
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na son ɗan wasan gaba na gefe na Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24, da kuma ɗan wasan gaba na gefe na AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 26, to amma kuma 'yan wasan biyu ba sa neman ƙulla wata sabuwar yarjejeniya. (Caughtoffside)
Bayern Munich ta shirya tattaunawa da Marc Guehi a kan yuwuwar ɗaukanshi, yayin da Tottenham za ta yi ƙoƙarin sayar da Yves Bissouma a watan Janairu, ita kuwa Aston Villa na duba yuwuwar mayar wa da Liverpool Harvey Elliot.
Darektan wasanni na Bayern Munich Max Eberl ya shirya tattaunawa da Guehi, a farkon watan Janairu, wanda shi ne lokacin da ɗan bayan na Ingila mai shekara 25 zai iya sanya hannu a yarjejeniya ta kafin ƙulla kwantiragi da wata ƙungiya ta waje saboda kwantiraginsa da Crystal Palace zai ƙare a bazara. (Sky Sports)
Tottenham za ta yi ƙoƙarin sayar da ɗan wasan tsakiya na Mali Yves Bissouma a watan Janairu, to amma saboda kwantiragin ɗan wasan mai shekara 29 zai ƙare a bazara, hakan zai iya sa a tsawaita kwantiraginsa da shekara ɗaya idan ƙungiyar ba ta samu mai sayensa ba. (Times)
Aston Villa ta sheda wa Liverpool cewa tana neman mayar mata da ɗan wasan tsakiya na tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 21 Harvey Elliot a watan Janairu. Tun a bazara Elliot mai shekara 22 ya tafi zaman aro Villa Park. (Teamtalk)
Kwamishinan gasar Amurka (Major League Soccer) Don Garber ya ce, za su yi maraba da Mohamed Salah a gasar idan ɗan gaban na Masar mai shekara 33 ya yanke shawarar barin Liverpool. (Fox Sports)
Ƙungiyar Stuttgart, ta Jamus na son ɗan gaban Real Madrid Gonzalo Garcia, duk da cewa ta san abu ne mai wuya ta samu ɗan wasan ma Sifaniya mai shekara 21. (Sky Sports)
Manchester United ta ce ba ta sha'awar ɗaukan tsohon ɗan wasan Sifaniya Sergio Ramos, wanda tun bayan da ya bar Monterrey ta Mexico a farkon watan nan ba shi da wata ƙungiya.(ESPN)
Bournemouth ta fahimci cewa ɗan wasan gaba na gefe na FC Basel Philip Otele, mai shekara 26, a matsayin wanda zai iya maye gurbin Antoine Semenyo. (Teamtalk)
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai