Nunez ya fara komawa kan ganiya a Liverpool - Slot

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Liverpool, Arne Slot ya ce sun fara amfana da Darwin Nunez, wanda yake lakantar ƙwazon da ake bukata daga gare shi a ƙungiyar.
Ɗan wasan tawagar Uruguay ya taka rawar gani a Carabao Cup ranar Alhamis da ta kai Liverpool ta yi waje da Tottenham da cin 4-0, duk da cewar bai ci ƙwalllo ba a wasan.
Waɗanda suka ci wa Liverpool ƙwallaye a karawar sun hada da Cody Gakpo da Mohamed Salah a bugun fenariti da Dominik Szoboszlai da kuma Virgil van Dijk.
Nunez ya yi kokari wanda Diogo Jota ya canje shi a gurbin mai cin ƙwallaye, daga baya aka sa Luis Diaz a matakin lamba tara.
Watakila Slot ya fara amfani da Jota a FA Cup da Liverpool za ta fuskanci Plymouth mai buga Championship ranar Lahadi.
Ya shiga wasa canji a karawa da Tottenham, ana fatan zai koma kan ganiya, sakamakon jinya da ta sa bai yi karawa huɗu ba.
Haka kuma ya yi zaman benci a karawar Premier League da Liverpool ta je ta doke Bournemouth a Premier League.
Rawar da Nunez ya taka a wasa da Tottentam na nufin ɗan wasan yana da makoma a Liverpool, yayin da Slot zai ke amfani da shi a gurbin da zai fi yin abin kirki.
Ana sa ran Slot zai yi sauye-sauye da yawa a fafatawar ranar Lahadi, domin manyan ƴan wasa su huta kafin karawar hamayya da Everton ranar Laraba.
Sai dai a wasan karshe a cikin rukuni a Champions League, Liverpool ba ta yi amfani da manyan ƴan kwallonta ba a karawa da PSV Eindhoven, wadda ta yi rashin nasara - karo na uku da aka doke ta a dukkan fafatawa a bana.
Liverpool wadda take ta ɗaya a kan teburin Premier League, za ta je Everton a wasan Premier League ranar Laraba.











