Makomar Rodgers, Pochettino, Allegri, Eriksen, Sancho, Zaha da Fatu

Asalin hoton, Getty Images
Leicester ta fara tattaunawa da kocinta Brendan Rodgers kan sabunta kwangilar shi saboda yadda Arsenal ta fara nuna sha'awa tana son dauko shi. (Telegraph)
Tsohon dan kocin Tottenham Mauricio Pochettino ba zai karbi aikin horar da Bayern Munich ba. (Bild - in German - subscription required)
Tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri ya ce ba zai koma aikin horar da 'yan wasan ba amma yana koyon Ingilishi yayin da ake tunanin zai koma Ingila domin karbar aikin horar da 'yan wasa. (ESPN)
Manchester United har yanzu tana fatan za ta dauko dan wasan Tottenham Christian Eriksen, mai shekara 27, a Janairu duk da dan wasan ya yi watsi da bukatar haka a bazara. (Mirror)
Chelsea na son karbo dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, mai shekara 27. (Independent)
Dan wasan Chelsea Olivier Giroud, mai shekera 33, yana da wahala ya bar kulub din a Janairu. (Sun)
Borussia Dortmund ba ta shirya rabuwa da dan wasanta na Ingila ba Jadon Sancho, mai shekara 19, har sai zuwa karshen kaka. (Telegraph)
Tsohon kocin West Ham da Newcastle da kuma West Brom Alan Pardew ya ce yana son karbar aikin horar da 'yan wasan Everton amma ya ce tsohon kocin kungiyar David Moyes ya fi dacewa. (Mail)
Wakilan dan wasan Faransa da ke taka leda a Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 22, sun gana da shugabannin Chelsea da Manchester City. (El Desmarque - in Spanish)
Matashin dan wasan Barcelona mai shekara 17 Ansu Fati ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya kuma an saka ma shi kudi fam miliiyan £337.5 ga duk kungiyar da ke son sayen shi. (FC Barcelona)











