Barcelona: Messi ya kafa sabon tarihin buga wasa

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya ci kwallo a wasansa na 700 a Barcelona yayin da kungiyar ta kai zagayen 'yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League bayan ta lallasa Borussia Dortmund.
Dan kasar Argentina wanda ya ci kwallo 114 a gasar, shi ne ya fi kowa jefa kwallo a raga a Barcelona.
Fasin din da ya bai wa Suarez ne ya taimaka wa Barca ta zira kwallon farko a wasan, sannan lafari ya ce an yi satar gida bayan ya bayar da wani fasin din an ci ta biyu.
Minti hudu bayan haka Messi ya kara ta biyun - kwallonsa ta 613 ga Barca - da kafarsa ta hagu daga yadi na takwas.

Asalin hoton, Getty Images
Antoine Griezmann ne ya ci ta uku daga wani fasin din na Messi, inda kwallon ta gangara raga ta bangaren dama.
Matashin dan wasan kasar Ingila Jadon Sancho ya farke wa Dortmund kwallo daya ana saura minti 13 a tashi daga wasa.
Barcelona ce ta daya a rukunin F da maki 11, sai Inter Milan da Dortmund a matsayi na biyu da na uku da maki bakwai kowaccensu da kuma Salvia Prague mai maki biyu a matsayi na hudu.
Yanzu wajibi ne Dortmund ta samu karin maki a wasanta da Slavia Prague sama da wanda Inter Milan za ta samu a wasanta da Barcelona ranar 10 ga watan Disamba - yayin da suke rige-rigen samun shiga zagayen 'yan 16.











