Champions League: Lionel Messi ya kusa kafa tarihi a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi zai kasance dan wasa na biyu da ya bugawa Barcelona wasanni 700, idan ya fito a wasan da kungiyar za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund ranar Laraba.
Dan wasan mai shekara 32, wanda ya ciyowa kulob din kwallaye 612, na gab da kamo tarihin da Xavi ya kafa na fitowa wasanni 767 a Barca.
Barca da Dortmund nasara suke nema a Camp Nou da za ta basu damar tsallakawa zagaye na 16.
Kocin Dortmund Lucien Favre na fuskantar matsin lamba yayin da kulob dinsa ke a mataki na shida a gasar Bundesliga.
Barca dai kakar bana a gasar Zakarun Turai bata nuna bajinta sosai ba duk da cewa tana sama a teburin La Liga. Kulob din ya samu damar kara matsawa gaba ne bayan da ya samu galaba daci 2-1 a kan Leganes ranar Asabar.
Kocin Barca Ernesto Valverde ya ce: "Barcelona, tana bukatar cin nasara, duk da cewa ta na iya bakin kokarinta."
"sai dai wani lokacin al'amarin yakan zo mana ne a ba zata.
Barcelona bata taba rashin nasara a hannun Borussia Dortmund ba a wasanninsu uku da suka yi a baya.
Barca dai ta samu galaba a kan Dortmund din sai kuma yi canjaras da suka yi a wasanni biyu.
Dan kwallon Barcelona Lionel Messi ya yi kokarin kai harin zura kwallo a raga sau 12 ba tare da nasara ba a wasannin Zakarun Turai da kungiyar ta karbi bakunci a kakar wasa ta bana.
Idan ya kasa cin kwallaye a kan Dortmund, zai zama karo na farko kenan tun a watan Oktoban 2011 da bai zura kwallo a raga ba sau uku a jere a wasan da Barcan ta karbi bakunci a gasar Zakarun Turai.











