Champions League: Frank Lampard yace yana da yakinin zasu samu galaba a kan Valencia

Chelsea ta isa Valencia ranar Talata

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Chelsea ta isa Valencia ranar Talata

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ce wasan su da zasu yi da Valencia a gasar Zakarun Turai na nufin ba zasuyi rashin nasara ba, ko da kuwa ba su samu abinda suke so ba.

Chelsea dai na mataki na biyu a saman teburin rukuni na takwas. Abinda take nema shine samun nasara a wasan domin tsallakawa zagaye na 16.

Kungiyar dai ta sha kaye da ci 1-0 har gida a hannun Valencia a zagayen farko na wasan rukuni.

Amma Lampard ya ce kayen da suka sha ne ya sanya suka shiga matakin da suke a saman teburi.

"Tawagarmu tana da kyau, sai dai ka yi wasarere da aikin ka to kuwa zaka gani a kasa. kuma abinda muke fuskanta kenan a halin yanzu", inji Lampard.

"Munyi kuskure sosai, amma zamu gyara."

Kungiyar zata yi wasanta ba tare da da wasa Callum Hudson-Odoi ba, kuma 'yan wasa irin su Ross Barkley da Antonio Rudiger basa cikin tawagar da zasu fafata a wasan nata da Valencia, duk da cewa sun fito a filin atisaye.

A wani labarin kuma, kocin Valencia Albert Celades ya ce kungiyar da zasu karbi bakuncinta na daya daga cikin manyan kungiyoyi da ke turai, don haka akwai aiki a gabansu.

Chelsea ta samu nasara a wasanninta 13 da tayi a dukkanin gasar da ta fito, ko da yake ta sha kaye a hannun Manchester City a wasansu da suka yi tattaki a gasar Premier.

Dukkanin kungiyoyin biyu na da maki bakwai a saman teburi tare da Ajax. Kuma kowannen su nasara yake nema a wasan da zai yi.