El Clasico: Madrid da Barca sun yi watsi da sauyin filin wasa

Bajon gasar La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin siyasa tsakanin gwamnatin Sifaniya da kuma 'yan aware na Catalonia ne ya shafi El Clasico

Zanga-zangar siyasa da kuma cecekucen da ake ta yi a yankin Catalonia ne ya jawo sauyin filin wasan da za a fara buga wasan El Clasico, sai dai wadanda abin ya shafa wato Real Madrid da Barcelona ba su amince da sauyin ba.

Tun farko dai BBC ta nemi ji daga kungiyoyin biyu domin karin bayani sai dai ta fahimci cewar ba a tuntube su ba kan batun.

Sai dai jaridar Marca ta kasar ta Sifaniya ta ruwaito cewa Real Madrid ta bukaci da a dage wasan ne zuwa wani lokaci daban maimakon sauya filin wasa idan har ana tsoron wani tashin hankali.

Kazalika, Barcelona ma ta ce lallai sai dai a buga wasan a filin wasan nata kamar yadda aka tsara tun farko.

A ranar 26 ga watan Oktoba aka tsara cewar Real Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na tara a gasar cin kofin La Liga a karawar hamayya da ake yi wa lakabi da a harshen Sifaniyanci El Clasico.

Bukatar ta mahukuntan La Liga ta zo da ba-zata ganin yadda duka kungiyoyin biyu suka yi mamaki da neman sauyin.

Real din dai tana ganin cewa ya kamata a bi abin da aka tsara tun farko domin yin adalci ga bangarorin biyu a wasannin La Liga ganin yadda da ma cen karawar ta El Clasico ke da tata yanayin na musamman.