Granada ta casa Barcelona, ta mai da ita ta 7 a teburi

Asalin hoton, Getty Images
Granada da ta hauro gasar La Liga a bana ta bai wa Barcelona, zakarun gasar, mamaki a wasan mako na biyar, inda ta makure ta da ci 2-0.
Ramon Azeez ne ya goga wa kwallo kansa a gefen turke minti biyu kacal da take wasa.
Sai bayan an dawo hutun rabin lokaci ne koci Ernesto Valverde ya sako Messi da matashin dan wasa Ansu fati, amma duk da haka Alvaro Vadillo sai da ya kara ta biyu a bugun finareti bayan Arturo Vidal ya yi laifi a cikin yadi na 18.
Wannan sakamako ya bar Barcelona tana reto a kasan Granada da maki uku wadda ita kuma ta dare saman teburin kafin wasa tsakanin Real Madrid da Sevilla a gobe Lahadi.
Yanzu Barcelona tana mataki na 7 ne yayin da ta gaza cin wasa a wasanninta na waje da ta yi har shida a La Liga.







