Barca ta taya Neymar £137m, Man U na son Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta yi tayin farko kan karbar aron tsohon dan wasanta Neymar kan fam miliyan 137, da nufin sayen dan wasan na Brazil mai shekara 27.
Amma Paris St-Germain ta yi watsi da tayin inda ta bukaci Barcelona ta biya fam miliyan 229. (Marca)
Manchester United ta ware fam miliyan 100 domin karbo dan matashin dan wasan Ingila Jadon Sancho wanda ke taka leda a Borussia Dortmund, s idan an sake bude musayar 'yan wasa a watan Janairu. (Sun)
Liverpool da Manchester City da Manchester United da Arsenal da kuma Chelsea suna cikin manyan kungiyoyin Turai da ke farautar dan wasan Bayer Leverkusen na Jamus Kai Havertz, mai shekara 20, wanda aka saka wa kudi fam miliyan 90. (Sport1 - in German)
Bayer Leverkusen na sha'awar karbar dan wasan baya na Liverpool Dejan Lovren, mai shekara 30 bayan ya kasa komawa Roma. (Bild - in German)
Tottenham na tattaunawa da Club Bruges domin sayar da dan wasan tsakiyarta Victor Wanyama, mai shekara 28, kan fam miliyan 11. (Telegraph)
Michy Batshuayi, mai shekara 25, na son ci gaba da taka leda a Chelsea, kafin bude kasuwar musayar 'yan wasa a Janairu. (Standard)
Manchester City na nazarin karbo matashin dan wasan Argentina Thiago Almada, mai shekara 18, bayan ya ki aminewa ya sabunta kwangilarsa da Velez Sarsfield. (A Bola, via Manchester Evening News)
Bayern Munich ta yanke shawarar sayar da dan wasan bayanta Jerome Boateng, mai shekara 30, kan fam miliyan 22. (Mail via Marca)











