Kayatattun hotunan Afrika: Daga 18 zuwa 24 Agustan 2023

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya

Short presentational grey line
Yar ƙasar Kenya Faith Kipyegon ta sake lashe zinari a tseren mita 1500 a wasannin duniya

Asalin hoton, Hannah Peters/Getty Images

Bayanan hoto, Yar ƙasar Kenya Faith Kipyegon ta sake lashe zinari a tseren mita 1500 a wasannin duniya
Tawagar Ethiopia ta yi nasarar dukkanin lambobin yabo a tseren gudun ƙarshe na mita 10,000 inda Sifan Hassan ta faɗi kafin cima layin ƙarshe

Asalin hoton, Aleksandra Szmigiel/Reuters

Bayanan hoto, Tawagar Ethiopia ta yi nasarar dukkanin lambobin yabo a tseren gudun ƙarshe na mita 10,000 inda Sifan Hassan ta faɗi kafin cima layin ƙarshe
A wani ɓangaren na duniyar wasanni a Afirka, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Algeria Islam Slimani ya samu tarba daga magoya bayan sabuwar ƙungiyarsa Coritiba ta Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wani ɓangaren na duniyar wasanni a Afirka, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Algeria Islam Slimani ya samu tarba daga magoya bayan sabuwar ƙungiyarsa Coritiba ta Brazil
Afirka ta Kudu ta karrama ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ta hanyar raye-raye na gargajiya a ranar Talata kafin soma taron Brics a Johannesburg.

Asalin hoton, Jacoline Schoonees/Reuters

Bayanan hoto, Afirka ta Kudu ta karrama ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ta hanyar raye-raye na gargajiya a ranar Talata kafin soma taron Brics a Johannesburg.
Shugaban China Xi Jinping shi ma ya halarci taron inda ya samu babbar lambar yabo daga shugaba Cyril Ramaphosa.

Asalin hoton, Alet Pretorius/Reuters

Bayanan hoto, Shugaban China Xi Jinping shi ma ya halarci taron inda ya samu babbar lambar yabo daga shugaba Cyril Ramaphosa.
an rawa Musa Motha ya ƙayatar a Johannesburg ranar Asabar, wanda ya rasa ƙafarsa tun yana yaro

Asalin hoton, Oupa Bopape/Getty Images

Bayanan hoto, Dan rawa Musa Motha ya ƙayatar a Johannesburg ranar Asabar, wanda ya rasa ƙafarsa tun yana yaro
A ranar Alhamis mawaƙin Rege na Nijar Black Mailer ya yi waƙa ta nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis mawaƙin Rege na Nijar Black Mailer ya yi waƙa ta nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki
Ko za a samu sauyi a Zimbabwe? Jami'an zaɓe na kaɗa ƙuri'a cikin duhu a ranar Laraba

Asalin hoton, KB Mpofu/Reuters

Bayanan hoto, Ko za a samu sauyi a Zimbabwe? Jami'an zaɓe na kaɗa ƙuri'a cikin duhu a ranar Laraba
Matasan Masaai a Kenya na nishaɗi tare da wani dattijo a ranar Juma'a lokacin bikin Eunoto na tabbatar balaga

Asalin hoton, Luis Tato/AFP

Bayanan hoto, Matasan Masaai a Kenya na nishaɗi tare da wani dattijo a ranar Juma'a lokacin bikin Eunoto na tabbatar balaga
Mabiya ɗariƙar Katolika tare da Fafaroma a fadar Vatican ranar Laraba

Asalin hoton, Alberto Pizzoli/AFP

Bayanan hoto, Mabiya ɗariƙar Katolika tare da Fafaroma a fadar Vatican ranar Laraba
Wasu mabiya addinin kirista suna nuna wata alama a hannunsu a wani bikin addini a Dronka, ƙasar Masar

Asalin hoton, Roger Anis/Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mabiya addinin kirista suna nuna wata alama a hannunsu a wani bikin addini a Dronka, ƙasar Masar
Bayan wasu kwanaki, ƴan Habasha a Tigray sun gudanar da bikin addini da suka saba duk shekara
Bayanan hoto, Bayan wasu kwanaki, ƴan Habasha a Tigray sun gudanar da bikin addini da suka saba duk shekara
...yayin da kuma wasu yara ke tuƙa kwale-kwale a wani ƙauye da ke kusa da Cotonou na ƙasar Benin a ranar Talata

Asalin hoton, Yanick Folly/Getty Images

Bayanan hoto, ...yayin da kuma wasu yara ke tuƙa kwale-kwale a wani ƙauye da ke kusa da Cotonou na ƙasar Benin a ranar Talata

Dukkanin hotuna suna da haƙƙin mallaka