Yadda dokar bai-daya kan aure da gado ta raba kan Indiyawa

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Soutik Biswas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent
Idan aka zo kan maganar da ta dangancin aure, saki ko gado da riƙon yaro, Indiya na da dokoki daban-daban tsakanin al'umominta wadanda ke mutunta addini da al'adunsu, abin da suka yi imani ko yarda da shi.
Amma ba da batun 'yanci ana ta tattaunawa kan wata doka da ake kira Uniform Civil Code a Turance ko UCC, doka ce da ta shafi dukkanin 'yan kasa ba tare da la'akari da addini ko jinsi ko yanayi tasowar mutum ko tarbiyya ba.
Kuma dokar ta kasa na son jihohi ta tabbatar kowa na bin wannan doka.
Amma dai dokar - na fuskantar turjiya daga wajen masu bin addini Hindu da Musulmi, masu rinjaye wato Hindu - sun ƙi sauyawa ko aminta da abubuwan da ke kunshe a dokar, batun da ya kai su har ga kotun koli.
Yanzu haka jam'iyyar BJP mai mulki ta Firaminista Narendra Modi na sake nazari kan batun.
Jihar Uttar Pradesh, da BJP ke mulki, da Himachal Pradesh da Madhya na tattaunawa kan dokar UCC.
Domin tabbatar da hakan, dokar UCC na daga cikin alkauran da BJP ke amfani da shi a gangaminta, da kuma batun gina wajen bauta a yankin Ayodhya da ake jayaya, da kuma wargaza matsayi na musamman da ake bai wa Kashmir.
Yanzu da ake ginin wajen bauta, da kuma ƙwace ikon gashin kai ga Kashinmir, batun dokar UCC ke sake jan hankali.
'Yan Hindu masu tsatsauran ra'ayi na bada misali da wadannan dokoki da suke ganin abu ne da ya shafi Musulmi - sun ba da misali da batun saki uku.
Tsarin rabuwar aure bisa musulunci a nan take - wanda gwamnatin Modi ta haramtaa a 2019. BJP ta ce ba za a taɓa samun daidaito ba muddin aka ci gaba da tafiya kan tsarin UCC.
Sai dai mai sharhi kan harkokin siyasa Asim Ali ya ce abin da ake tunani na tattare da sarkakiya.

Asalin hoton, AFP
A wani batun kuma, ana ganin rungumar tsarin UCC na iya sake haifar da wani rikicin ko a tsakanin Hindu masu rinjaye a kasar, da BJP ke cewa tana wakilta.
Dokar UCC na iya tarwatsa 'yancin walwala ga Hindu da kuma Musulmi," a cewarsa.
Irin wadanan dokoki na da wahalar gaske wajen hada kan 'yan kasa musamman a kasa irin Indiya.
Duk da cewa Hindu na mutunta wasu tsarin al'adu, suna kuma mutunta dokoki da al'adun wasu al'umomin na jihohi daban-daban.
Sannan akwai dokokin Musulunci da ba kowa ke bi ba - akwai wasu masu ra'ayin Sunni Bohra, da misali, ke amfani da wasu dokokin Hindu idan aka zo kan batun gado da neman maye gurbi.
Sannan akwai dokoki daban-daban na jihohi daban-daban idan aka zo kan batun 'yancin dukiya da kadarorin gado.
Jihohin da Kiristoci suka fi rinjaye kamar Nagaland da Mizoram na da nasu dokoki da ya tafi daidai da al'adunsu ban da addini.
Goa na da al'adu kamar 1867 da ke aiki kan kowanne al'umma sai dai akwai bambance-bambance ga mabiya Katholika da wasu mutanen, ciki harda wanda ke bai wa kabilar bigamy kariya daga Hindu.
Irin wadannan dokoki na da alaka da abubuwan da mutane suka yarda da shi kama daga gwamnatin tarayya da jihohi.
Tun a shekarun 1970 jihohi ke yin dokokinsu. Shekaru kafin shekara ta 2005 gwamnatin Hindu tayi kwaskwarimar da ke bai wa 'ya'ya mata damar samun gado kai guda da maza, akwai jihohi biyar da suka soma amfani da tsarin.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu idan aka dubi yadda dokokin jihohi ke tasiri a batutuwan da suka shafi mutane kai-tsaye.
A dau batun riƙon ɗa. A bisa al'adar Hindu, ana shiga riƙon ɗa saboda dalilai na addini ko akasin haka - domin samun ɗa namiji da zai gaji kadarori ko kuma wanda zai jagoranci yin jana'iza ga iyayensa.
A wani ɓangare kuma, ba a yarda da irin wannan tsari a addinin Islama ba.
Sai dai India ita kanta na da tsarin doka da ke bai wa 'yan kasa damar riƙo, ba tare da la'akari da wani addini ba.
Sannan ƙwararu na lalube kan dalilan dokokin riƙo da abin da ya sa ake matsawa a kansu.
"Wadanne tsare-tsare ake bi - Hindu, Musulmi ko Kirista?," Kwarare Alok Prasanna Kumar, na wata kungiya mai zaman kanta a Bangalore ya yi sharhi:
Ya ce UCC dole ta amsa wasu tambayoyi na 'yan ci: Menene tsarin yin aure da sakin aure?
"Menene hanyoyin daukan yaro domin riko da kuma abubuwan da ka iya biyo baya? Mene ne yanci rabon dukiya idan maganar saki ko rabuwar aure? A karshe, menene dokokin gadon kadarori?
Wannan batu na tattare da siyasa, wanda ka iya je ya dawo wa mutum, a cewar Mista Ali.
Ya za a yi gwamnati BJP ta amince da doka iri guda da ke amincewa da tsarin aure tsakanin addinai da al'umomi da ke adawa da wasu tsare-tsarenta da kuma ke kokarin mara baya ga dakile aure tsakanin mabiya addinai daban-daban?
Ko jam'iyyarsa ce, kamar yadda Mista Ali ke zargi, kokarin kawo dokoki a kananan jihohi ba tare da takurawa al'adu ba na mutanenta?

Asalin hoton, Getty Images
Ba abin mamaki ba ne, ita kanta kotun koli ta nuna daburcewa kan UCC.
A hukunci daban-daban cikin shekaru 40 da suka gabata, ta bukaci gwamnati ta bijiro da doka da za ta tabbatar da ginuwar kasa da ci gabanta.
A 2018, an kafa hukumar da ke bai wa gwamnati shawarwari kan batutuwan shari'a a kan dokar.
UCC dai ba wai harsashi take dannawa ba. Batu ne na hadin kan kasa da bin dokoki da tsarin kudin tsarin mulki, a cewar Mista Kumar.
Domin shawo kan matsalar daidaiton jinsi kan irin wadannan dokoki babu wata matsala ko laifi a yiwa dokar kwaskwarima, a cewar kwararu.
Hakan na iya sa a samu ko a rungumi tsarin da zai daɗaɗawa kowa.
Mista Ali na da yaƙinin cewa akwai jihohin da BJP ke mulki da har yanzu ke bibbiyar batun dokar UCC ba wai saboda neman suna ko ƙarin ƙuri'u ba.
"Wani kokari ne na sake gina kanta a siyasa, da tabbatar da cewa akwai tsari na mutunta juna tsakanin addinai da Hindu ba.
Wasu dai na lalube don sanin ko me ne dalilin da ya sa BJP ta gaggara bijiro da tsari a jihohi duk da cewa ta jima kan mulki.
Babban zabe dai na tafe nan da shekara biyu, shin jam'iyyar na ganin lokaci ya zo ne?
"UCC dai a yanzu ita ce batun da ake tada jijiyoyin wuya a kai, kuma muhawarar da ake tafka a yanzu ba ta siyasa ba ce. A soma gabatar da daftarin dokar tunkunan, a cewar Mista Kumar."











