Na taba sayar da motata na je London don shiga shirin Ra'ayi Riga na BBC - Dr Bashir

Dr Bashir

Asalin hoton, DR Bashir

Bayanan hoto, Dr Bashir Ibrahim malami a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Kano, wanda ya ce ya sayar da motarsa ya biya kudin zuwa London don ya ziyarci cibiyar BBC.

Wani zai yi mamakin wace irin soyayya ce ta wata kafar yada labarai da za ta sa mutum ya sayar da kadararsa don zuwa ganinta.

Sai dai gani ya kori ji, wannan shi ne abin da wani masoyin BBC Hausa ya taba yi a 'yan shekarun baya, don kawai ya je ya ga wannan kafa da yake tsananin so.

A shekarar 2019 ne Dr Bashir Ibrahim malami a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Kano, ya sayar da motarsa ta hawa ya biya kudin tafiya birnin London don ya samu ziyartar cibiyar BBC.

Baya ga haka kuma ya samu cikar burinsa na shiga cikin filin Ra'ayi Riga da BBC Hausa ke gabatarwa a duk ranar Juma'a da daddare.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 11 ga watan Maris din 2022 a filin Ra'ayi Riga da aka yi na musamman don murnar cikar sashen shekara 65 da kafuwa.

Ba shi kadai ba, mutane da dama da suka shiga shirin sun bayyana irin tsawon lokacin da suka dauka suna bin shirye-shiryen BBC a rediyo da talabijin da intanet da kafafen sada zumunta.

Masu sauraro daga kasashe da dama sun shiga filin kamar daga Sudan da Libiya da Saudiyya da Amurka da Birtaniya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma nan Najeriya.

Cikin wadanda suka bayyana labaran ban mamaki har da wanda cikin sunansa da yake amfani da shi a hukumance har da inkiyar BBC.

A ranar Lahadi 13 ga watan Maris ne BBC Hausa ta cika shekara 65 da kafuwa.

Na sayar da motata na je BBC London

Dr Bashir Ibrahim ya ce tun bai san kansa ba ya fara saurarar BBC a 1979.

"A lokacin ina makarantar sakandare. Kuma a lokacin idan ina son jin labarin manyan jam'iyyu a BBC nake samu.

"Dalilin BBC ne na ji son yin karatun jami'a daga digiri na farko har na biyu zuwa na uku."

"Dalilin sauraron BBC ne ya sa da na zo bincikena na karatun jami'a na yi a kan auren Hausawa.

"Dalilin BBC ne kuma ya sa na sayar da motata na je Turai don na ziyarci BBC.

"Kuma na je din har na samu shiga shirin Ra'ayi Riga don ina matukar son shirin.

"Kuma Allah ya ba ni sa'a an yi shirin Ra'ayi Riga da ni a kan aure. Na kuma ga BBC gidan rediyo gari guda.

"Sannan kuma aka karramani sosai a BBC. Kuma ina son gaya wa mutane cewa duk iliminka idan ba ka jin kafofin yafa labarai irin su BBC to an bar ka a baya.

"Ni BBC ta bude min kwakwalwa sosai."

Sunana BBC

bbc

Kabiru BBC Dala ya ce sunan gidan rediyon ya shiga jerin sunayensa tun lokacin yana makarantar sakandare abokansa suka sa masa saboda iya karatun Hausa da ya yi.

"Ana yawan sanya ni karatun Hausa a gaban asambili saboda na iya sosai, sai dalibai ke ce min BBC.

"Tun daga lokacin BBC ya shiga cikin sunayena kuma duk takarduna har da fasfo na tafiya hakan ne a ciki," in ji shi.

Hon Nasiru Muhammad dan siyasa a Kano wanda ya shiga cikin shirin kai tsaye a ofishinmu na Landan ya ce tun yana jami'a a 1982 ya fara saurarar BBC.

"Ni da BBC mun zama jini da tsoka don har akwai mutane na kusa da ni da ke cewa sai an min addu'a don ganin yadda na makalewa BBC.

"Duk inda nake duk abin da nake ina kula da lokaci don na saurare su," in ji shi.

'BBC ta zama kishiyar matata'

Abdurrahaman

Shi ko Abdurrahman Abdullahi Ringim cewa ya yi saboda tsabar kulafucin BBC har matarsa na kishi da ita.

"Ko hira mutane ke min a lokacin da nake saurarar BBC sai ta ce musu ku kyale shi ba za ku samu kansa ba don yana sauraron wannan matar tasa (BBC) tukunna."

Malam Abdullahi daga karamar hukumar Ungogo ya ce ya shafe kusan shekara 50 yana sauraron BBC kuma har yanzu bai daina ba da karamar rediyonsa.

"Shirin Duniya Ina Muka Dosa ya bude min kwakwalwa ta wajen sanin duniya da sassanta sosai," in ji shi.

Da jin haka ne ma sai shi Abdulrahman ya yi alkawarin aika masa wayar zamani don ya dinga samun saukin sauraron sashen a zamanance.

Tuna baya

Yawanci masu sauraron sun yi ta tuno da tsofaffin shirye-shiryen sashen na da, da ma na yanzu.

Sun ambato shirye-shirye irin su Labarina da Rana Mai Kamar Ta Yau da Dadina da Kasata da Da Ina da Zabi da Filin Wasiku da Kwartanniya da Haifi Ki Yaye da sauransu.

Wata mai sauraro Maman Khairat ta ce "lokacin ina makarantar sakandare, da zarar mahaifina ya kunna BBC zan bar duk abin da nake in zo sauraron shirin BBC Hausa.

"Akwai wani shiri da Jamila Tangaza ke yi a lokacin mai suna Labarina. Har yanzu ina tuna wasu daga cikin labaran," in ji ta.