Arewa24 ta buɗe sashen wasannin kwaikwayo da fina-finai

Kwana Casain

Asalin hoton, Arewa24

Tashar Talabijin ta Arewa24 ta sanar da cewa ta ƙirƙiri sabon sase da zai ringa tsara ƙagaggun fina-finai da wasannin kwaikwayo na labaran Najeriya da Afirka ta yamma a harshen Hausa da kuma Turancin Ingilishi.

Sashen shi ne zai ringa rubutawa da tsarawa da kuma jagorantar wasannin kwaikwayon da fina-finai.

Wata sanarwa da tashar ta Arewa24 ta fitar ranar Talatar nan 08 ga watan Fabrairu 2022, ta ce tuni sashen ya shirya wasu fitattun fina-finai a harshen Hausa da suka karɓu a Najeriya da Yammacin Afirka kamar "Dadin Kowa" da "Kwana Casa'in".

Sanarwar wacce tashar ta fitar ranar Talata ta ce a yanzu haka sabon sashen yana aiki kan wasu sabbin fina-finai, haka kuma tashar ta Arewa24 za ta fara nuna wani shirin talabijin na musamman irinsa na farko zuwa ƙarshen shekarar nan, kamar yadda shugaban tashar Jacob Arback ya bayyana.

Ya ce tashar tana horar da wasu fitattun marubata ƴan Najeriya da masu shirya fina-finai, da masu bayar da umarni da taurari tun daga lokacin da aka ƙaddamar da tashar shekara takwas da ta gabata.

Sanarwar ta ce Evans Ejioju shi ne shugaban sashen, kuma shi ne yake shirya fim ɗin Kwana Casa'in tun lokacin da aka fara. Sauran shugabanin sashen sun haɗa da Salisu Balarabe da wasu ƙwararru da za su ringa sa ido kan yadda ake shirya fina-finan tashar.

Arewa24

Asalin hoton, Arewa24

Shugaban tashar ta Arewa24 Mista Arback ya ce nan gaba suna fatan haɗa kai da fitattun masu harkar fina-finai na duniya sannan suna fatan nan gaba fina-finansu za su samu karɓuwa a faɗin nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.