Australia ta kori Novak Djokovic saboda rashin riga-kafin korona

Reuters

Asalin hoton, Reuters

An mayar da Novak Djokovic gida daga Australia bayan ya yi rashin nasara a wata dama ta karshe da wata ko tu ta ba shi na sauraren kokensa a kasar.

Alaƙalan sun yi watsi da bukatar dan wasan tennis din da yaƙi amincewa a yi masa rigakafin, bayan da gwamnati ta soke bizarsa kan abin da ta ce "domin kare lafiyar sauran mutane".

Novak Djokovic ya ce bai ji dadin abin da ya faru ba, amma ya amshi wannan hukunci. ya kuma fice daga kasar ne a jirgin sama ida ya nufi Dubai.

Hakan dai ya kawo karshen turka-turkar da aka kwashe kwana 10 ana yi, wadda dan kasar Sabiyan ya so ya yi amfani da ita domin kare kambunsa na gasar Australian Open.

Gwamnatin kasar ta ce halayyar dan wasan mai shekara 34 ta kasance mai hatsari ga sauran 'yan kasar.

Novak Djokovic during a practice session

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Novak Djokovic

A dalilin wannan hukuncin, Djokovic ba zai sami damar kare kambunsa a karo na goma a gasar Australian Open da za a fara ranar Litinin a birnin Melbourne na kasar ba.

A ranar ta Litinin aka shirya cewa zai buga wasansa na farko.

Yayin zaman kotun na ranar Lahadi, lauyoyin Mista Djokovic sun kasa gamsar da alkalai ukun da suka saurari bahasi cewa matakan gwamnatin kasar ba su da tushe.

Tun ranar 6 ga watan nan na Janairu ake tsare da Djokovic a wani otel na musamman a birnin Melbourne - wurin da hukumar shige da fice ta kasar ke tsare wadanda ba su da izinin shiga kasar - wanda kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da shi daga kasar.