Iyayen yara a Zamfara sun ce 'ya'yansu sun fara manta karatu

Dalibai

Iyayen yara a jihar Zamfara da ke arewa masoyammacin Najeriya, sun yi kira ga gwamnati da ta dubi yi wuwar bude makarantu don hana dalibai ci gaba da gararamba kan titi.

Makarantun firamare da na sakandare a jihar sun kasance a rufe kusan wata biyu, a wani bangare na tsaurara matakan yaki da 'yan bindiga da suka bullo da salon satar dalibai a makarantu.

Tun a ranar 1 ga watan Satumbar 2021, ne gwamna Bello Muhammad Matawalle, ya sanar da rufe makarantu, kama daga firamare har sakandare, ya Allah jeka ka dawo ko na kwana da ke fadin jihar.

Hakan ya biyo bayan zafafa kai hare hare a makarantun sakandare har ma da na gaba da su.

Matakin gwamnatin na daukar wannan mataki ya zo ne jim kadan bayan sace daruruwan daliban makarantar sakandare da ke Kaya a karamar hukumar Maradun.

Kuma harin ya zo ne kasa da mako guda bayan sako daliban kwalejin kimiyyar noma da kiwo da ke Bakura.

Tuni dai wasu iyayen yara suka fara nuna fargaba kan yadda ba bu wani bayani da ke fitowa daga bakin hukumomin jihar kan batun bude makarantu, duk da samun haske a yaki da 'yan bindigar.

Wani mahaifin daya daga cikin daliban da ke karatu a jihar ta Zamfara ya shaida wa BBC cewa, 'yarsu har ta fara manya karatu, kuma ganin haka a yanzu shi da mahaifiyar yarinyar ne ke koyawa 'yar ta su karatu a gida.

Mutumin ya ce, yakamata gwamnati ta dubi wannan yanayi da dalibai a jihar ke ciki, domin in banda gararanba ba bu abin da wasu daliban ke yi.

Ita ma wata mata da BBC ta ji bakinta a kan rashin bude makarantu a jihar ta Zamfara, ta ce yakamata gwamnatin jihar ta su ta kalli abin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wajen bude makarantu duk da satar daliban da ake yi a jihar.

Matar ta ce," Gwamnatinmu ta dauki mataki irin Kaduna, a samar da tsaro a makarantu sannan sai a bude su don yara su ci gaba da karatu".

To kowanne hali makarantu masu zaman kansu ke ciki a Zamfara?

Makarantu masu zaman kansu na jin jiki ta fannin samun kudin shiga a jihar ta Zamfara.

A tabakin wani mai irin wannan makaranta, ya ce ya kamata a lalubo wata hanya daban ta yakar 'yan bindiga, a maimakon kulle makarantu da ka iya mummunar illa ga al'umma da kuma tattalin arziki a nan gaba.

Mutumin ya ce su ma kansu masu irin wadannan makarantu suna cikin halin ka-ka-ni-kayi, a don haka ya bukaci gwamnatin jihar data duba lamarin.

Ko me gwamnatin jihar Zamfara ta ce game da bude makarantu?

BBC ta tuntubi kwamishinar ilimi ta jihar, Zainab Lawal Gumi, don jin matakin gwamnati game da batun bude makarantu, in da ta ce ba wai sun rungume hannuwa ne kawai ba bayan rufe makarantu, akwai matakan da ake dauka na bude.

Ta ce," Akwai kwamiti na musamman da aka kafa don bincike da samar da mafita a kan bude makarantu, kuma yanzu muna kokarin samar da kwakkwaran tsaro a dukkan makarantun kafin a kai ga sanya ranar da za a bude su".

Kwamishinar ta ce nan bada jimawa ba za a sanar da matakan da aka dauka na bude makarantu dama ranar komawa makaranta.

Matakin rufe makarantu a Zamfara Daya ne daga matakan tsaurara fada da 'yan bindiga a jihar, in da yanzu haka garin Gusau ne kawai ake iya buga waya ko hada hadar kudi a bankuna saboda katse sadarwa.

Bugu da kari kasuwannin mako mako na ci gaba da zama a rufe, wanda hakan ka iya mummunan tasiri ga tattalin arziki.

To amma da dama sun yi na'am da wadannan matakai, matsawar hakan zai samar musu da zaman lafiya.