Alec Baldwin: Wata mata ta mutu bayan harbinta da jarumi ya yi da bindiga a fim

Alec Baldwin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alec Baldwin is a co-producer of the film Rust, which was being filmed in New Mexico
Lokacin karatu: Minti 2

Wata mata ta mutu wani mutum guda kuma ya jikkata bayan jarumi Alec Baldwin ya harba bindiga a wajen daukar wani fim a jihar New Mexico.

Jami'an 'yan sanda a Amurka sun ce Mista Baldwin ya yi harbin ne lokacin da ake daukar fim din.

Matar mai suna Halyana Hutshins, an garzaya da ita aisibiti a jirgi amma ta mutu sanadin raunukan da ta ji. Sai kuma daraktan shirin Joel Souza wanda ke kwance a bangaren kulawar gaggawa.

Kakakin Mista Baldwin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa harba bindigar shirin aka yi ba daidai ba.

Hutchins mai shekara 42 na cikin tawagar mutanen da ke lura da hotuna a shirin. Shi kuma Souza mai shekara 48 an dauke shi ne a motar asibiti kai tsaye, sai dai har yanzu ba a bayyana halin da yake ciki ba.

Sai dai har yanzu 'yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a Bonanza Creek Ranch, wani fitaccen wuri da ake yawan daukar fim a wurin.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ta fitar, ya ce Mista Baldwin ya yi magana da masu bincike.

"A radin kansa ya tattauna da masu binciken a cikin ginin da suke bayan ya gama kuma ya kama gabansa," in ji kakakinsa.

Kamar yadda yake a bayyananta na shafukan sada zumunta Hutshins 'yar Ukraine ce kuma ta tashi a sansanin sojin Soviet da ke Arctic Circle.

Ta karanta aikin jarida a birnin Kyiv, da kuma Fim a Los Angeles, a kuma 2019 mujallar Amurka ta Cinematographer ta bayyana sunanta a matsayin matashiyar da take haskakawa.

Ita ce daraktar daukar hotuna ta fim din Archenem a 2020, wanda Adam Egypt Mortimer ya ba da umarni.

"Ban ji dadin mutuwar Halyna ba," in ji Mortimer.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

A wata sanarwa da kungiyar shirya fina-finai ta duniya ta fitar ta ce mutuwar Hutchins ta matukar kada su, kuma babban rashi ne.

"Har yanzu babu wasu tartiban bayanai, amma abubuwa za su bayyana nan ba da jimawa ba, kuma muna goyon bayan a gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari," in ji shugaban kungiyar John Lindley da kuma daraktarta Rebecca Rhine.

Mista Baldwin shi ne wanda ya dauki nauyin shirin, kuma ya sanya wa fim din takwara, wani dan shekara 13 wanda jikansa ne da baya jin magana wannan ya janyo kisan tsau-tsain da aka samu.

Duka 'yan uwansa hudu jarumai ne, Baldwin ya fito a fina-finan talabijin masu yawa inda ya taka rawa daban daban tun daga shekarar 1980,

Ya lashe kyaututtuka da dama a matsayinsa na Jack Donaghy a wani fim din NBC 30 Rocks. Kuma kwaikwayon da yake yi akan Donald Trump ya kara daukaka shi tare da samun kyautuka masu yawa, ciki har da ta Emmy wadda ya ci a karo na uku.

Irin wannan lamarin kisan a wajen daukar fim abu ne da bai fiye faruwa ba, ba a fiye jin sa ba.

Akan yi amfani da makaman gaskiya a yayin daukar fina-finai, amma ana sanya mata hasashi tamkar na gaske - domin yarika kara kamar na gaske.

A 1993, Barndo Lee - mai shekara 28 wanda da ne a wajen Bruce Lee- shi ma ya mutu a lokacin da ake daukar wani fim The Crown, inda aka yi irin wannan harbi na tsautsayi kuma ya mutu take.