Covid-19: Korona ta yi mummunar ɓarna cikin makon jiya a Afirka

Asalin hoton, AFP
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce yawan mutanen da ke kamuwa da cutar korona da waɗanda suke mutuwa sanadin cutar korona na matuƙar ƙaruwa a Afrika.
Hukumar ta ce ta kaɗu da alƙaluman mutanen da ke mutuwa sanadin cutar Korona a nahiyar, inda ta ce ba a taɓa samun mace-macen korona kamar na makon jiya tun bayan ɓullar annobar.
Kawo yanzu, sama da mutum 6,400 ne suka mutu dalilin annobar korona, adadin da ba a taɓa gani ba cikin mako guda.
Ƙwararru a fannin lafiya na bayyana damuwa kan ƙaruwar mace-mace da kuma yawan masu kamuwa da cutar korona kullum a nahiyar, inda suka ce sabon nau'in cutar na Delta wanda ke da saurin yaɗuwa na ƙara bayyana a ƙasashen Afirka da dama.
Haka kuma, sun nuna fargaba kasancewar ƙasa da kashi 2 cikin 100 na mutanen nahiyar ne kawai suka yi riga-kafin korona.
Farfesa AbdusSalam Nasidi, tsohon jami'i a hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Afrika ya ce wannan matsala ba ta rasa nasaba da sakacin hukumomin ƙasashen Afrika.
"Ba sa tsayawa su mai da hankali kan matakin da ya kamata a ɗauka na yin riga-kafi, yadda za mu iya rage lahanin da wannan ƙwayar cuta za ta yi a nahiyar," a cewarsa.
Farfesa Nasidi ya ce hukumomin sun rage ayyukan wayar da kan al'umma game da riga-kafin, da yadda ya kamata su kare kansu daga kamuwa da cutar.
Ya kuma ce ƙasashen Afrika suna jan ƙafa wajen sama wa ƴan ƙasarsu allurar riga-kafin.
"Duk duniya yanzu abin da ake nema kenan, amma kasashen Afrika da yawa har yanzu ba su sayo wannan allurar da kansu ba. Sun dogara da sadaka daga manyan ƙasashen duniya," in ji shi.
Farfesa Nasidi ya ce babban tashin hankali shi ne sabbin nau'o'in cutar kobid-19 da ke ƙara bayyana inda ya ce kawo yanzu an samu nau'i bakwai tun bayan ɓullar cutar a shekarar da ta gabata.
Ya ce duk da yake duka nau'o'in na iya janyo wasu cutukan da ma mutuwa, sai dai ya ce nau'in da ya fi ɗagawa masana kamar shi hankali shi ne Delta mai saurin yaɗuwa tsakanin matasa da ƙananan yara ga kuma saurin kisa.

Asalin hoton, Getty Images
WHO ta ce babu shakka yaɗuwar nau'in Delta mai saurin bazuwa ta taimaka wajen ƙaruwar masu cutar da yawan waɗanda suka mutu a faɗin nahiyar.
Kawo yanzu, an samu nau'in Delta a sama da ƙasashe 17 na Afrika kuma WHO ta ce nahiyar na fuskantar ɓarkewar annobar a karo na uku.
Afirka ce ta baya a duniya wajen yin allurar riga-kafin cutar korona kuma Farfesa Nasidi ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba samun ƙaruwar masu cutar dole ne gwamnatocin kasashe su dauki matakin kulle.
Ya ce "Ko ba a sa dokar kulle a ko ina ba, wuraren da cutar ta fi ƙamari dole ne a sa dokar a nan, don a tabbatar ba ta ci gaba da yaɗuwa ba."
Ya ce idan ba haka ba kuwa, akwai yiwuwar komawa ƴar gidan jiya, wato sa dokar kullen a duka faɗin ƙasashen.











