Cutar korona ta yi ajalin mutum 400,000 a Indiya

Kididdigar jami'an lafiya a India ta nuna sama da mutum dubu 400 cutar korona ta yi ajali a kasar.
An kai wannan adadi ne bayan samun mutuwar mutum 853 cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Harwayau kididdigar ta nuna a kowacce rana cikin kwanaki biyar a jere, sama da mutum dubu 50 ne ke kamuwa da cutar a Indiya.
Sai dai kwararru sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu ka iya fin haka, sakamakon yadda wasu ke mutuwa a gida ba tare da hukumomi sun san da hakan ba.
Har wa yau, an sake gargadi kan yiwuwar barkewar cutar a karo na uku. Sabon nau'in cutar korona samfurin Delta da ya bulla a kasar Indiya na saurin yaduwa, inda kawo yanzu ya fara shiga wasu kasashe ciki har da Birtaniya da Afurka ta Kudu.
Indiya ce kasa ta uku a duniya da yawan masu cutar korona. Ko a watan Maris da ya wuce kasar ta yi fama da karancin iskar shaka ta Oksijin, lamarin da ya kara janyo asarar rayuka tun ma kafin akai mutane asibitocin da sukai cikar kwari saboda marasa lafiya.







