An far wa cibiyar riga-kafin korona a Pakistan

Daruruwan mutane ne suka far wa wata cibiyar lafiya ta gwamnati da ake yin riga-kafin cutar korona a babban birnin Pakistan wato Islamabad.
Yawancin mutanen ma'aikata ne a kassahen waje ko matafiya da ke son a yi musu riga-kafin cikin gaggawa.
Ganau sun shaida wa BBC cewa gungun mutanen sun yi wa babbar kofar gilshi ta shiga cibiyar tsinke, saboda tsoron ka da allurar ta kare alhalin ba a yi musu ba.
Kasar Saudiyya da yankin Gabas Ta Tsakiya, sun bukaci ma'aikata 'yan ci-rani su tabbatar an yi musu riga-kafin cutar korona ta kamfanin AstraZeneca da Pfizer, wanda ake da karancinsu a kasar ta Pakistan.
Miliyoyin 'yan Pakistan ne ke aiki a kasashe daban-daban na duniya, sannan kudaden da suke aikowa gida na da matukar muhimmanci ta fuskar bunkasa tattalin arzikin kasar.
Har yanzu cutar korona na ci gaba da barna a kasar Pakistan, ya yin da a ban gare guda kuma ake nuna damuwa kan halin da makofciyar kasar Indiya ke ciki sakamakon bullar sabon nau'in cutar mai suna Delta, da jami'an lafiya suka ce mai hadarin gaske ne da saurin yaduwa ga kuma yi wa wanda cutar koronar ta ci karfi kwaf daya.







