Yadda yanar gizo-gizo ta mamaye kan tituna a Australiya

Asalin hoton, CAROLYN CROSSLEY
Wasu manyan yanar gizo-gizo sun bayyana tare da zarge tsakanin bishiyoyi da kewaye su a kusa da wasu garuruwan kasar Australia da suka fuskanci ambaliyar ruwa a baya-bayan nan.
Mazauna yankin Victoria's Gippsland sun ce yanar gizo-gizon masu kama da mayafai sun bayyana ne bayan kwanaki kadan da aka shafe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.
A wani yanki, yanar gizo-gizon da lullube fiye da kilomita daya na kan wata hanya.
Kwararrun sun ce wadannan yana masu kama da mayafai sun faru ne saboda kokarin tsira da rai da ake kira "ballooning", inda gizo-gizo ke jefa igiyar sililki don kokarin hawa kan tudu.
Dr Ken Walker, wani kwararre a fannin lura da halittun kwari daga gidan ajiyar kayan tarihi na Victoria, ya ce akwai yiwuwar cewa miliyoyin gizo-gizo sun jefa zirin siliki zuwa sama kan bishiyoyin da ke kewaye.
"Gizo-gizon da ke rayuwa a kan dandamalin ƙas ana bukatar tashi zuwa sama cikin sauri. Silikin kan yi toroko zuwa sama su makalae a jikin shue-shuken kuma za su iya tsira,'' ya shaida wa jaridar The Age.

Asalin hoton, CAROLYN CROSSLEY
Wannan ya haddasa bayyanar abubuwa masu kamar mayafai da suka lullube dausayin da ke tsakanin garuruwan Sale da Longford.
'Kamar igiyar ruwa na karkadawa'
Wata kansilar yankin Carolyn Crossley, ta ce ta sauka kasa zuwa madatsar wani tafki ne a ranar Litinin don duba barnar da ambaliyar ruwan da ta faru ta haifar, kawai sai ta yi kicibis da wannan al'amari.
Mis Crossley ta ce ta taba ganin irin haka amma ba mai tsananin yawa irin wannan ba.
"Bai zama abin tsoro ba- ya yi matukar kyau. Komai a lullube cikin wannan mayafi mai kyau na yanar gizo-gizon, sun mamaye bishiyoyi da shingaye,'' ta shaida wa BBC.

Asalin hoton, CAROLYN CROSSLEY
"Lokacin rana na daf da faduwa kuma hasken ya yi matukar kyau, dubi yadda suke kadawa, wannan abu mai kama da fasalin igiyar ruwa na a fadin wurin.''
Ta ce yanar sun bayyana a yanayi na falle daya ne inda kananan gizo-gizon ke bi ta kai.
"Ganin yadda suke a hade duka ba su rabu da juna ba - hakan ya nuna cewa wadannan gizo-gizo sun hada kai wajen tsara wannan basira ta hada yanar,'' ta ce.
Wata mazauniyar yankin Amanda Traeger, ta shaida wa BBC cewa iyalanta sun yi zaton yanar sheka ce a bakin hanya.
"Na taba gani amma ko kusa ba kamar wannan ba,'' ta ce. '' Gaskiya akwai ban sha'awa.''
Nan gaba kadan ne a cikin wannan makon ake sa ran wadannan yanar gizo-gizo za su katse.
Mazauna yankin sun ce wadannan abubuwan ban mamaki na da kyaun kallo, bayan da suka shaida mummunan ambaliyar ruwa a cikin kwanaki kadaan da suka gabata.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da isak mai karfin gaske sun mamaye wurare da dama na yankin Victoria, tare da haddasa ambaliyar ruwa da barna a makon da ya gabata.
An gano gawawwakin mutane biyu a cikin motocinsu a wuraren ambaliyar ruwa biyu.
Mahukunta sun bayyanaa guguwar a matsayin wani babban bala'i, kuma daruruwan gidaje a kasar sun kasance babu wutar lantarki.











