Zaftarewar laka da ta kashe hanyoyin intanet a Najeriya

Asalin hoton, CHAMAREL MARINE SERVICES (CMS)
Masana kimiyya na kawo rahoton wata zaftarewar laka ta ƙarƙashin ruwa mafi tsawo da aka taɓa gani.
Zaftarewar ta faru ne a ƙarƙashin teku kusa da Afrika ta Yamma, a wani kogo mai zurfi da ruwa ke gudana a cikinsa a kusa da Kogin Congo.
Ana tunanin ƙasa da laka na nisan kilomita ne suka zaftare a cikin kogon.
Wannan ƙasa da taɓo masu yawan gaske sun ci gaba da tafiya tsawon kwanaki biyu kuma nisan kilomita 1,100 a ƙarƙashin Tekun Atlantika.
Ba dan zaftarewar ƙasar ta tsinka wasu manyan wayoyin sadarwa biyu da ke ƙasan ruwa ba, da ba a san da ita ba. Hakan ya janyo naƙasu a harkar intanet tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.
Kuma saboda ilimin masu binciken da suka jera kayan gwaji a ilahirin faɗin Kogon Congo, da ba a san zaftarewar ta auku ba.
"Muna da jering wayoyi da lamarin ya shafa, ya tsinka su kuma ya fizgo su daga ƙarƙashin ƙasa don haka masu sa ido nan da nan suka aiko mana saƙonnin email," a cewar farfesa Peter Talling na Jami'ar Durham da ke Burtaniya.
Ƙasa da taɓo sun riƙa gudana da gudun gaske. Kuma da ya ke suna raruke gaɓar teku a lokacin da suke tafiya sai su yi ta ƙara gudu," ya shaida wa BBC.
Zaftarewar ƙasar ta ƙarƙashin ƙasa ta fara ne ranar 14 ga watan Janiarun shekarar da ta gabata. Amma sai yanzu aka bayyana aukuwarta saboda masana kimiyya sun buƙaci lokaci su tattara bayanai.
Tawagar ta ce abubuwa biyu ne suka janyo lamarin.
Na farko shi ne ambaliyar ruwa mai yawan gaske da aka yi a Kogin Congo a ƙarshen watan Disambar 2019. A kan yi ambaliyar ruwa a nan ne sau 1 cikin shekaru 50, don haka sai ta ɗabi ƙasa da taɓo da dama ta ganganra da su ƙarƙashin ruwan da ke gudana a kogon nan. Amma wannan ya faru ne mako biyu kafin zaftarewar ƙasar.

Abin da ya biyo baya a watan Janairu shi ne igiyar ruwa mai girman gaske.
"Nan da nan ruwan ya cakuɗe da kasar nan da taɓo daga ƙasa-ƙasan tekun kuma wannan ya haifar da ƙara wa ruwan nauyi," a cewar Farfesa Dan Parsons na Jami'ar Hull.

Asalin hoton, IMAGE COPYRIGHTICPC-UNEP 2009 CABLES REPORT (CARTE
Tawagar ta yi binciken farko-farko kan gudun ruwan ta hanyar lura da lokacin da na'urorinsu suka bayyana.
An gano cewa gudun ruwan mai haɗe da laka da farko ya kai mita 5.2 duk daƙiƙa ɗaya a saman kogon amma da ya ci gaba sai ya kai mita 8 duk daƙiƙia ɗaya a lokacin da ya kai bakin kogon.
Farfesa Talling da abokan aikinsa sun bayyana wannan a wata maƙala da aka rubuta.
Akwai muhimman darussa kan yadda za a magance wannan.
Babu shakka ba zai yiwu a iya yin hasashen lokacin da zaftarewar laka zata auku, amma sanin wasu abubuwa dangane d bubuwan da ke haifar da ita na iya yin tasiri kan inda za a riƙa jera wayoyin sadarwa da jiragen ruwa na gyaransu a faɗin duniya.
An gyara wayoyin sadarwar biyu da suka tsinke a tsakiyar watan Janiarun 2020 cikin ƴan makonni. Amma an samu ƙarin wayoyin da suka tsinke da zaftarewar kasar ta ci gaba.
Wani abu mai jan hankali da aka gano dangane da abin da ya sa wasu wayoyin suka tsinke wasu ba su tsinke ba ya danganta ne da rarukuwar da ƙasa ta yi a hanyar ruwan.
A wasu wurare, gudun ruwan taɓo zai raruko ƙarƙashin teku yayin da a wasu wuraren kuma sai dai taɓon ya danƙare da yawansa a ƙarƙashin ruwan.
Wannan binciken na Congo shi ne na farko da ya gano wannan al'amari.

Da wuya a iya jaddada alfanun rukunin wayoyin sadarwa da ke ƙarƙashin ruwa na ƙasa da ƙasa.
Sama da kashi 99 cikin 100 da duka intanet da ke tsakanin nahiyoyi na tafiya ne ta cikin waɗannan wayoyin, ciki har da aika kuɗi da ake yi kullum da yawansu ya kai tiriliyan ɗin dala.
Binciken a aka gudanar a Kogon Congo ya samu sa hannun ɓangarori da yawa ciki har da hukumar IFREMER a Faransa da Cibiyar GEOMAR Helmholtz mai bincike kan teku a Jamus.
Wannan binciken ya samu jangorancin kamfanonin sadarwa na Durham da Angola.

Asalin hoton, IMAGE COPYRIGHTTYCO TELECOMMUNICATIONS











