Afirka Ta Kudu ta dakatar da yin alluran riga-kafin coronavirus

Corona testing centre

Asalin hoton, Reuters

Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ta dakatar da aikin yi wa al'ummarta alluran riga-kain korona samfurin da AstraZeneca ke samar wa wanda aka shirya fara rabawa cikin makon nan.

Hakan ya biyo bayan wani nazari da ya tabbatar cewa riga-kafin ba shi da tasiri kan nau'in kwayar cutar da ya bayyana a Afirka Ta Kudu.

Babban jami'in kimiyya da ke kula da nazarin ya ce yana iya zama kariya ga wadanda ke fama da matsalar cutar korona mai tsanani, amma sai an sake gudanar da wani binciken.

Amma ya bayyana cewa allurai miliyan ɗaya na allurar riga-kafin AstraZeneca da suka isa kasar a makon jiya za su lalace idan ba a yi amfani da su ba nan da watan Afrilu.

Afirka Ta Kudu ta shirya yi wa ma'aikata lafiya miliyan 1.2 alluran a matakin farko, amma wannan nazarin ya kawo cikas kan shirin.

Gwamnatin kasar ta dakatar da yin alluran bayan da ta bayyana cewa riga-kafin ba zai iya bayar da kariya ba ga ƙwayar cutar na Afirka Ta Kudun.

Afirka Ta Kudu ta yanke hukuncin komawa kan wani riga-kafin da kamfanin Johnson & Johnson da Amurka ke haɗawa, wanda nazarin da aka yi ya nuna yana da tasiri sosai kan sabon nau'in ƙwayar cutar.