Covid: Masu cutar korona sun zarce miliyan daya a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Afirka ta Kudu ta zama ta farko a nahiyar Afirka da masu dauke da cutar korona a cikin kasar suka zarce miliyan daya.
Wannan labarin mara dadin ji na zuwa ne bayan da wani sabon nau'i na kwayar cutar korona ya bayyana a cikin kasar.
Wasu asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya sun sanar da gagarumin karuwar masu rashin lafiya, wanda ke dagula lamura.
Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa zai sanar da wasu matakai masu tsauri domin hana kwayar cutar ci gaba da yaduwa.
Ministan lafiya na Afirka ta Kudu Zweli Mkhize ne ya sanar da samun wannan adadin, inda kawo yanzu aka samu mutum 1,004,413 da suka kamu daga cutar Covid-19, kuma mutum 26,735 suka sun mutu tun da annobar ta barke a watan Maris.
A makon jiya kawai Afirka ta Kudu ta sanar da mutum 11,700 sun kamu da cutar - karuwar kashi 39 cikin 100 daga makon da ya gabaci wannan - kuma daga Laraba zuwa Juma'a, an sami mutum sama da 14,000 da ke kamuwa a cikin kowace rana.

Asalin hoton, Reuters
Wani sabon nau'i na Covid-19 - wanda masana suka lakaba wa suna 501.V2 - ake zaton shi ke kama 'yan kasar da yawansu.
An dai gano shi ne yayin da wata hadaka ta masana kiwon lafiya na Afirka ta Kudu suka bankado sabon nau'in a lardin Eastern Cape inda ya rika bazuwa zuwa wasu sassa na kasar.
After South Africa, the worst hit country on the African continent is Morocco which has seen 432,079 cases and 7,240 deaths. They are followed by Egypt with 131,315 cases and 7,352 deaths and Tunisia with 130,230 infections and 4,426 deaths.











