Masarautar Zazzau: 'Abin da ya sa har yanzu ba a naɗa sabon sarki ba'

Asalin hoton, Zazzau Emirate/facebook
Zaɓen sabon Sarkin Zazzau ya gaji ɗaukar lokaci, kamar yadda masana tarihin masarautar suka bayyana.
A makon da ya gabata ne dai aka yi jana'izar margayi Dr Shehu Idris wanda ya rasu bayan shafe fiye da shekaru 45 a kan gadon Sarauta.
Yanzu haka kuma ƴan Najeriya sun zura ido don jiran sanarwa daga gwamnatin jihar na sabon Sarkin Zazzau da zai gaji marigayi Dr Shehu Idris.
Masana tarihin Masarautar Zazzau sun ce akwai dalilai da suka sa ake samun jinkiri wajen sanar da sabon sarkin Zazzau.
Masanin tarihin Dakta Shu'aibu Shehu, daraktan cibiyar bincike da ajiye kayyakin tarihi ta Arewa House a Kaduna ya ce, tsaikon da aka samu na sanar da sabon sarkin zazzau ba sabon abu ba ne a masarautar Zazzau.
Ya ce a duk lokacin da aka ce sarkin Zazzau ya rasu, zaben sabon Sarkin Zazzau ya kan ɗauki zafi sosai domin a cewarsa "saboda gidajen da suka gaji sarautar ko wannensu yana so sarautar ta koma gidansu, kuma ba kasafai ake gaggawa ba wajen naɗa sabon sarki."
Masanin ya ƙara da cewa wannan ba wani abu ba ne sabo domin kasancewar Masarautar Zazzau daya da ta ƙunshi gidajen masarautu guda hudu da suka cancanta a zaɓi sarki.
"Ana daukar lokaci domin samo jajirtacce da ƙwararre, ba sai an yi gaggawar zaben sarki ba," in ji masanin.
Ko an taba samun jinkiri kafin sanar da sabon Sarkin Zazzau?

Asalin hoton, Zazzau Emirate/Facebook
An ɗauki lokaci kafin sanar da naɗa Sarkin Zazzau Jafaru da Sarkin Zazzau Shehu Idris.
Masanin tarihi Dakta Shu'aibu Shehu ya ce sai bayan kwana 14 da mutuwar Sarki sannan aka sanar da naɗa Sarkin Zazzau Jafaru a ranar 15 ga watan Fabrairun 1937.
Kuma ko lokacin da Sarkin Zazzau Muhammad Aminu ya rasu a Landan ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 1975, ba a naɗa Shehu Idris ba sai ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar.
Lokacin da aka zaɓi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris sai da aka jira ƴan majalisar sarki suka zauna suka tantance suka zaɓi waɗanda suka cancanta sannan suka tura wa majalisar sarakuna ta arewa, wacce kuma ta tura wa gwamna wanda kuma ya sanar da wanda aka zaɓa.
Wane hali ake ciki
Bisa tsarin sarautar Zazzau ana zaɓen sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda huɗu - wato daga Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sulluɓawa.
Akwai kuma majalisar masu zaɓen sarkin Zazzau ta mutum biyar da za su zauna su tantance waɗanda suka cancanta kuma rahotanni sun ce sun miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna sunayen mutum uku da gwamna zai zaɓi ɗaya a matsayin sabon sarki.
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ne zai zaɓi sabon Sarkin Zazzau, cikin mutum uku daga cikin ƴaƴan gidan masarautar Zazzau da masu naɗin sabon sarki suka tura masa.
A makon da ya gabata gwamna El-Rufa'i ya ce yana karanta wasu littafai kan sarautar Zazzau domin yi masa jagora wajen fahimtar yadda zai nada sabon sarki.
A yayin da Gwamna El-Rufai ke ci gaba da karatu, 'yan Najeriya kuma na ci gaba da zuba ido domin ganin ranar da za a nada sabon sarkin Zazzau.











