Zamantakewa a Japan: Mutanen da ake ɗaukar haya domin su kashe aure

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Christine Ro
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC WorkLife
A 2010, an yanke wa Takeshi Kuwabara hukuncin zaman gidan yari sakamakon samunsa da laifin kashe masoyiyarsa, Rie Isohata. Sai dai abin da mutane suka fi mayar da hankali a kai shi ne Kuwabara ɗan wakaresaseya ne - wani ƙwararre da mijin Isohata ya ɗauka haya domin kashe musu aure.
Masu sana'ar wakaresaseya sun shahara ne wajen raba aure tsakanin mata da miji ko kuma raba dagantaka tsakanin saurayi da budurwa.
Wakilin ƙungiyar wakaresaseya wato Kuwabara, yana da aure da 'ya'ya, kuma shi ne ya nemi Isohata su tattauna a wani babban kanti. Ya fake kan cewa ba shi da aure kuma shi injiniya ne a ɓangaren kwamfuta, inda irin kayan da ya saka yayin tattaunawar tasu mutum zai ɗauka da gaske ba shi da aure.
Su biyun sai suka fara shiri wanda daga baya soyayyar da ke tsakaninsu ta zama mai ƙarfi matuƙa. Sai dai a wani ɓangaren, abokin aikin Kuwabara ya ɗauki hotonsu a wani otel, inda mijin Isohata ya yi amfani da waɗannan hotuna a matsayin shaida na yin saki. (Ana neman irin wannan shaidar idan za a yi saki a Japan.)
Bayan Isohata ta gano cewa Kuwabara ƙarya ya yi mata, sai ta fusata inda ta nemi su rabu. Saboda Kuwabara ba ya son su rabu, sai ya shaƙe mata wuya da igiya.
Bayan shekara guda sai aka tura shi zaman gidan yari na shekara 15.
Masana'antar wakaresaseya
Masana'antar wakaresaseya ta yi ƙaurin suna bayan kisan da aka yi wa Isohata, da kuma wasu laifuka na almundahana. Wannan abin da ya faru ya ja aka yi gyara ga masana'antar ciki har da bayar da lasisi.
Sai dai Yusuke Mochizuki wanda jami'in "farewell shop" ne ya bayyana cewa illar da hakan ya jawo ta haɗa da raguwar tallata wakaresaseya a shafukan intanet, da kuma rashin aminci da jama'a ke nuna wa masana'antar wanda hakan ya zama babban ƙalubale ga jami'an wakaresaseya yayin da suke so su yi aikinsu.
Sai dai bayan kusan shekara 10 da mutuwar Isohata, an ci gaba da samun tallace-tallace a shafukan intanet, kuma masana'antar wakaresaseya na kasuwancinta yadda ya kamata duk da tsada da kuma matsalolin da ke cikin harkar.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu abin da kasuwar wakaresaseya ta sa gaba shi ne kashe aure. Wani bincike da aka yi ya gano cewa masana'antun wakaresaseya 270 na yin talla a shafukan intanet.
"Aikin da wakaresaseya ke yi na da tsada matuƙa," in ji Mochizuki, wani tsohon mawaƙi wanda ya sauya aikin da yake yi na ɗan sanda mai bincike zuwa aikin wakaresaseya.
Ya bayyana cewa zai iya amsar fam 2,970 a matsayin kuɗin haya ga lamarin da bai da wahala musamman idan yana da bayanai kan wanda ake so a far wa, amma a cewarsa, zai karɓa fiye da hakan idan wadda za a tunkara ba mai son mutane ba ce.
Ya bayyana cewa zai iya karɓar kuɗi da suka kai fam 145,000 idan wanda ke neman a yi masa aikin fitaccen mutum ne ko ɗan siyasa wanda hakan na buƙatar sirri mai ƙarfi.
Ci gaba da kasancewar masana'antar wakaresaseya na nuna cewa ana saka kuɗi da ƙarya cikin soyayya ba tare da mutane sun gane ba.
Wata marubuciya Stephanie Scott ta rubuta littafi mai suna What's Left Of Me, wanda littafin ya mayar da hankali ne kan batun Isohata.
Ta yi bincike matuƙa kafin ta wallafa littafin wanda hakan ya ja aka saka ta cikin ƙungiyar lauyoyi ta Japan.

Asalin hoton, Doubleday
Amincewa da saki
Scott ta bayyana cewa ɗaukar wakaresaseya haya na taimakawa wajen rage rigima gaba da gaba tsakanin miji da mata. Hanya ce ta kawo ƙarshen yanayi mai tsanani ba tare da rigima ba.
Kuma matar mutum za ta fi saurin karɓar takardar saki sakamakon ta samu wani da take so su ci gaba da rayuwa tare. Amma hakan zai iya zama yana da amfani idan ɗaya daga cikinsu bai amince da sakin ba, wanda hakan zai iya rikita al'amura.
Amma akasarin kwastamomin Mochizuki ba masu aure bane da suke so su rabu da matansu, sai dai yawancinsu masoya ne waɗanda suke so su rabu.

Asalin hoton, Julius Honnor
Rabuwa
Misali, bari mu ce Aya ta san cewa mijinta Bungo yana soyayya da wata a waje. Sai ta je ta samu jami'in wakaresaseya mai suna Chikahide.
Chikahide zai fara ne da bincike kan duk wasu bayanai da Aya ta bashi, da bin diddiƙin duk inda Bungo ke zuwa, da kuma duba irin wainar da yake toyawa a shafukan sada zumunta da sanin irin abokansa.
Zai ɗauki hotonsa domin nuna cewa lallai yana yaudarar matarsa. Bungo yana yawan son zuwa motsa jiki inda ya ke zama a garin Kagoshima, wannan ne ya sa Chikahide ya tura wani jami'in masana'antar namiji wanda yake da harshe irin na mutanen Kagoshima mai suna Daisuke, domin su haɗu.
Bayan lokaci kaɗan sai Daisuke ya fara zuwa wurin motsa jikin da Bungo ke zuwa, inda ya fara jan shi da labari domin su fara aminantaka. Binciken da Chikahide ya yi ya sa Daisuke ya samu bayanai sosai kan wane ne Bungo, wanda hakan ya sauƙaƙa masa wurin kawo zantuttuka da za su sa Bungo ya ji daɗi inda hakan ya zamana kamar su biyun sun san juna da daɗewa.
A hakan dai a hankali har ya samu labari sosai kan budurwar Bungo mai suna Emi.
Bayan Daisuke ya gama sanin Chiahide, sai ya kawo wata jami'ar wakaresaseya mai suna Fumika. Kamar yadda Daisuke ya samu bayanai daga wurin Bungo a wurin motsa jiki, Fumika sai ta fara shiri da Emi inda ta samu bayanai sosai a kanta, ciki har da labari kan saurayinta da kuma soyayyar da ke tsakaninsu.
Ba daɗewa ba sai Fumika ta haɗa liyafar cin abincin dare tare da Emi da sauran jami'an wakaresaseya. Ciki har da wani jami'i mai suna Goro.
Goro ya tattara bayanai sosai kan abin da Emi take so da abinda ba taso. Goro sai ya fara neman Emi da soyayya (sai dai a gaske Mochizuki ya ce jami'an wakaresaseya ba su kusantar kwastamominsu domin jima'i da su donn gudun karya dokar ƙasar ta karuwanci).
Sai da aka yi amfani da jami'ai huɗu na kusan tsawon watanni hudu kafin raba Bungo da budurwarsa.
Sakamakon Emi ta fara soyayya da wani, sai ta rabu da Bungo. An ci nasara matuƙa a wannan lamarin.
A hankali Goro ya zo ya rabu da Emi batare da ta san shi jami'in wakaresaseya bane .











